Hukumar kula da ingancin magunguna ta Pakistan (DRAP) ta amince da amfani da allurar rigakafin COVID-19 ta kamfanin Sinopharm na kasar Sin a mataki na gaggawa, yayin da ake samun karuwar masu kamuwa da cutar a kasar.
Ministan kula da harkokin kimiyya da fasaha na kasar, Chaudhry Fawad Hussain, ya shaidawa Xinhua cewa, an amince da sayen alluran rigakafin na Sinopharm ne saboda amincinsa da rahusa. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CRI Hausa)