Hukumar zabe Mai zaman kanta ta Jihar (KANSEIC) tace Jam’iyyar PDP na cikin jam’iyyun da suka tsaida ‘yan takarkaru a zaben Kananan Hukumomi da za’a gudanar ranar 16 ga watan Janairun Shekara ta 2021 a Jihar Kano.
Jawabin haka ya fito daga bakin shugaban Hukumar zaben Jihar Kano Farfesa Garba IIbrahim Sheka alokacin taron fadakarwa da aka shiryawa kungiyoyin da zasu sa ido a zaben da za’a gudanar a Jihar Kano.
Farfesa Garba IIbrahim Sheka yace Jam’iyyar PDP na cikin jam’iyyun 12 da suka tsayar da ‘yan takarkarun kujerun Shugabannin kananan Hukumomi 44 da Kuma Kansiloli 484.
“WanibTsagi na Jam’iyyar ta PDP ne ya gabatar da ‘yan takarkarun, kuma bamu samu wata sanarwar daga Kowa ne mutum ba dake nuna kauracewa zaben,” inji shi
A cewarsa, Hukumar na yin aiki tare da hadin guiwa da jami’an ‘Yan Sanda da kuma sauran Hukumomin tsaro domin tabbatar da sahihin zabe.
Gudanar da Ingantacce kuma gudanar da sahihin zabe hakki ne da ya rataya a wuyan masu ruwa da tsaki da jami’an tsaro gimshikai ne na samun nasarar zaben.
“Don Haka muke neman goyon bayan kowa da kowa domin gudanar da sahihin zabe a Jihar Kano.”
Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya bukaci Masu sa ido a harkokin zaben da su tabbatar da aikin sa idon kan harkar zaben tare da bayar da kyakkyawan rahoto ga Hukumar zaben domin samun nasarar kyakkyawan Shirin zabe na gaba.
Shi ma a nasa jawabin Shugaban muryar kungiyoyi Masu zaman kansu (CSOs) a Jihar Kano Ibrahim Waiya cewa ya yi an tsara taron ne domin fadakar da mahalarta taron shirye shirye kan aa Ido a harkar zaben.
Waiya ya ci gaba da cewa, an tsara Shirin tare da hadin guiwa tsakanin Hukumar zaben ta KANSEIC, CSOs da kungiyoyi Masu zaman kansu (KCSSR).
“Masu Sa’ido ba za su ahgala da neamn ganin laifi bane, aikinmu shi ne dubawa. Dole mu kasance bamu karkata ga kowane bangare ba,” inji Waiya.
Idan ba a manta ba tsagin Jam’iyyar PDP karkashin Jagorancin tsihon Gwamnan Jihar Kano Injinya Rabiu Musa Kwankwaso sun nesanta kansu da wannan zabe, ya yinda bangaren tsohon Minista Alhaji Aminu Bashir Wali suka tsayar da ‘yan takarkaru alokacin zaben.