Jam’iyyar PDP ta yi kira da a gaggauta kama Kwamishinan Zaben Jihar Adamawa, Malam Hudu Yunusa Ari, tare da gurfanar da shi gaban kuliya bisa laifin sanar da sakamakon zabe ba bisa ka’ida ba ga ‘yar takarar jam’iyyar APC, Aisha Binani, a matsayin wacce ta lashe zaben gwamnan jihar.
Jam’iyyar PDP a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Hon. Debo Ologunagba, ya kuma bukaci INEC, da ta umarci jami’in zabe da ya kammala tattara sakamakon zaben, sannan ya bayyana dan takararta, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben.
- Da Dumi-Dumi: Tambuwal Ya Lashe Kujerar Sanatan Sakkwato Ta Kudu
- Da Dumi-Dumi: INEC Ta Dakatar Da Tattara Sakamakon Zaben Gwamnan Adamawa
Jam’iyyar PDP ta zargi Kwamishinan zaben Jihar Adamawa da cewa jam’iyyar APC da ‘yar takararta sun yi wa jam’iyyar magudin zabe domin su yi amfani da su, duk da kuri’un da al’ummar Jihar Adamawa suka kada.
“Jam’iyyar PDP ta yi kira ga al’ummar Jihar Adamawa da ‘yan Nijeriya da sauran kasashen duniya da su yi watsi da sakamakon da aka bayyana.
“Abin da ya fi zama wauta abin da kwamishinan zaben Jihar Adamawa ya yi.
“Wannan mataki da Mallam Yunusa Ari ya dauka na yin zagon kasa ne kuma an yi la’akari da shi don haifar da rikici a Jihar Adamawa, ya lalata dimokuradiyyarmu da zaman lafiya a matsayin kasa,” in ji PDP.
PDP ta dage cewa matakin da ya dauka na zagon kasa ne da kuma haifar da rikici a jihar da kuma kawo cikas ga dimokuradiyya da zaman lafiya a matsayin kasa.