Jam’iyyar PDP ta dakatar da shugaban jam’iyyar a Jihar Ebonyi, Okorie Tochukwu Okoroafor, bisa zargin yi mata zagon kasa.
Kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP na kasa, ya dauki matakin ne a taron gaggawar da ta gudanar a ranar Juma’a, 27 ga watan Janairu, 2023.
- An Kama Wani Da Ake Zargi Da Hannu A Harin Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja
- Dan Gwamnan Jihar Nasarawa Mai Shekaru 36, Hassan Sule Ya Rasu
Ta ce dakatarwar ta zo ne bayan da aka yi nazari sosai kan halin Okoroafor da kuma ayyukansa a matsayinsa na shugaban jam’iyyar na Jihar Ebonyi.
Dakatarwar ta zo ne sa’o’i 24 bayan jam’iyyar PDP ta gudanar da yakin neman zabenta na shugaban kasa a jihar.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa, Hon. Debo Ologunagba, ya ce “Duba da sashe na 29 (2) (b) da 57 (3) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP, ta amince da dakatarwar a madadin kwamitin zartarwa na kasa ya yi wa Okorie Tochukwu Okoroafor daga yau Juma’a 27 ga watan Junairu, 2023, kan zargin yin zagon kasa.
“Saboda haka, Okoroafor an mika shi ga kwamitin ladabtarwa na jam’iyya don ci gaba da daukar mataki.”
Dakatar da Okoroafor ya biyo bayan dakatar da ‘yan jam’iyyar da aka yi a baya-bayan nan saboda wasu ayyukan da suka saba wa jam’iyyar.
A makon da ya gabata ne jam’iyyar ta dakatar da Sanata Chimaroke Nnamani da kuma wasu jiga-jigan jam’iyyar na Jihar Ekiti kan kin shiga sabgogin jam’iyyar.