Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Bauchi (BASIEC), ta ayyana jam’iyyar PDP da ke mulki a jihar, a matsayin wadda ta lashe dukkanin kujerun zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin jihar.
Zaɓen wanda aka gudanar a gundumomi 323 da suke faɗin jihar da jam’iyyun siyasa guda bakwai suka shiga aka dama da su a ranar Asabar.
- Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato
- Lokuta Da Yawa Nakan Dakata In Yi Kuka Ma’ishi Kafin Na Ci Gaba Da Rubutu – Fatima Gurin
Da yake sanar da sakamakon zaɓen a daren ranar Asabar, shugaban hukumar Ahmed Makama, ya ce za su miƙa shaidar lashe zaɓe ga zaɓaɓɓun a ranar Lahadi.
Ya sanar da cewa za a sanar da waɗanda suka lashe zaɓen kansiloli 323 a jihar daga baya, sai dai ya ce jam’iyyun adawa sun samu nasara a kujerar kansiloli uku, yayin da PDP ta lashe dukkanin sauran.
Waɗanda suka kasance zaɓaɓɓun su ne: ƙaramar hukumar Alkaleri Hassan Garba Bajama (shugaba), Abbas Ibrahim (mataimaki); Bauchi Mahmoud Baba Maaji (shugaba), Adamu Muazu Luda (mataimaki); Bogoro – Lawi Yakubu Sumi (shugaba), Markus Masoyi Mulki (mataimaki); Dambam- Yakubu Garba Tela (shugaba), Iliya Isah (mataimaki); Darazo – Sama’ila Yau Sade (shugaba), Amina Musa (mataimaki); Dass – Muhammad Abubakar Jiboa matsayin shugaba yayin da aka zabi Isah Abdulmumini Hanakuka a matsayin mataimakin sa; Gamawa Madaki Ahmed Gololo shugaba Umar Yakubu (mataimaki); Ganjuwa Mohammed Idris Miya (shugaba), Saleh Ahmed (mataimaki).
Sauran su ne: Giade Usman Muhammad Saleh (shugaba) Bahijja Auwalu (mataimaki); Itas Gadau -Hajara Jibrin Gidado (shugaba), Shuaibu Ahmad (mataimaki); Jama’are -Hon. Inuwa Abdullahi (shugaba), Saleh Muhammad (mataimaki); Katagum – Yusuf Babayo Zaki (shugaba), Misbahu Ibrahim (mataimaki) Kirfi – Abdulkadir Umar Dewu (shugaba), Mohammed Mohammed Bashir (deputy); Misau – Salisu Hussaini (shugaba); Moh’d Garba (mataimaki).
Sauran kuma su ne Ningi – Nasiru Zakarai (shugaba), Isah Mohammad (mataimaki); Shira – Abdullahi Ibrahim Beli (shugaba) Adamu Usman (mataimaki); T/ Balewa – Sama’ila Wakili Lere (shugaba), Maigari Ahmed (mataimaki); Toro -Pharm. Ibrahim Abubakar Dembo (shugaba), Adamu Umar Danyaro (mataimaki); Warji – Aminu Barmini (chairman), Habib Idris Usman (mataimaki), yayin da kuma Zaki – Adamu Yakubu (shugaba) da mataimakinsa Ibrahim Chiroma.