A ranar Lahadi kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta lallasa Heartland FC ta Owerri da ci 2-1 a wasan mako na 19 na gasar cin kofin kwallon kafa ta Nijeriya (NPFL).
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya rawaito cewa an buga wasan ne ba tareda yan kallo ba a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano biyo bayan takunkumin da aka kakabawa Pillars na biyan tarar Naira miliyan 12.
- Dan Kwallon Kano Pillars Ya Zazzaga Kwallaye Biyar A Ragar Gombe UnitedÂ
- Kano Pillars Ta Doke Rivers United A Kano
Dan wasan Kano Pillars, Suleiman Idris, ne ya ci kwallon farko a minti na 47 da fara wasa, yayin da Rabiu Ali ya kara ta biyu a minti na 85.
Clement Ogbobe ne ya ci wa bakin kwallo daya tilo a cikin mintunan karin lokaci ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp