Kasar Morocco ta kafa tarihin zama kasar Afrika ta farko da ta fara kai wa zagayen kusa da na karshe a Gasar Cin Kofin Duniya.
Hakan ya biyo bayan doke tawagar kasar Portugal da ci daya da babu a zagayen kusa dana kusa dana karshe.
- Wakilin Sin Ya Yi Kira Da A Dage Takunkumin Hana Shigo Da Makamai Da Aka Kakabawa DRC
- Sin Da Saudiyya Abokai Ne Na Gaskiya Bisa Manyan Tsare-tsare
Dan wasa El-Naysiri ne ya ci wa Morocco kwallonta da kai a minti na 43 na fara buga wasan.
Duk da cewa kasar Portugal ta kai munanan hare-hare amma har aka tashi ba ta iya farkewa ba, kuma a karshen wasan an bai wa Morocco jan kati dab da a tashi wasa bayan da da dan wasan gaba Ceddari ya karbi jan kati bayan an bashi katin gargadi har sau biyu saboda keta da ya yi.
Idan anjima ne za a fafata wasa tsakanin Ingila da Faransa kuma duk kasar da ta samu nasara za ta kece raini da Morocco.
A yanzu Maroko za ta buga wasan kusa da karshe da duk wanda ya yi nasara tsakanin Faransa da Ingila yau da daddare.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp