• English
  • Business News
Friday, October 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ra’ayi: Ba Na Shakkar Gwabzawa Da Kowa A Takarar Gwamnan Gombe – Mailantarki

by Sulaiman
3 years ago
Mailantarki

Ayau shafinmu na ra’ayi ya tattauna ne da Aliyu Suleiman inda ya ce, mai gidan shi Khamisu Mailantarki dan takarar gwamna a jam’iyyar NNPP baya shakkun fitowa takara da Gwamna mai mulki, ko kuma gwamnatin da ke kan mulki.

 

Wannan kuwa ba abin mamaki ba ne, domin a baya Mailantarki ya nuna cewa shi mutum ne mai jama’a. Su kuma jama’a su ne kasuwa, ba yawan rumfuna ba.

 

“A baya abu ne mai wahala a fito yin kokawar gaba-da-gaba da gwamna mai mulki a Jihar Gombe. Amma yanzu abu ne mai sauƙi, kuma idan mu ka yi gaba-da-gaba, mu ka haɗa ƙwanji a ranar zaɓe, to kayar da gwamna abu ne mai sauƙi a wuri na.” Inji Mailantarki, bayan an tsayar da shi takarar gwamna a ƙarƙashin NNPP.

LABARAI MASU NASABA

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya

 

Daga cikin laƙanin da Mailantarki ke taƙama da su, akwai jama’a, waɗanda su ne ya ce su ka roƙe shi ya fito takarar gwamna, domin su sake yi masa irin ruwa da ƙanƙarar yawan ƙuri’un da su ka taɓa yi masa a 2011. Wannan karon ma gaba ɗayan jihar ce, ba wai a ƙananan hukumomi 3 kamar na zaɓen 2011 ba.

 

Wani laƙanin da Mailantarki ya ce ya ke taƙama da shi, shi ne iƙirarin sa cewa gwamnatin APC ba ta tsinana wa Gwambawa abin a zo a gani har a yaba ba.

 

Ba wai girma ake buƙata ga wuƙar da za a feɗe giwa ba, a’a, mai kaifi ake nema komai ƙanƙantar ta.

 

Yayin da ake gwabza yaƙin neman zaɓen gwamnoni a faɗin jihohin Najeriya, zaɓen da zai kasance cikin sahun gaba wanda za a yi kallon kwatagwangwamar kokawa a Arewa, shi ne zaɓen gwamnan Jihar Gombe, wanda a cikin ‘yan takara har da Khamisu Mailantarki, wanda jam’iyyar NNPP ta tsayar takarar gwamna a Gombe.

 

Kada mai karatu ya yi shakku, tababa ko tantama cewa Mailantarki zai iya kayar da Gwamna Inuwa Yahaya a zaɓen 2023. Wanda bai san Mailantarki ba, shi ne zai tsaya ya na wasiwasin wannan nazari.

 

A zaɓen 2011, Mailantarki ya fito takarar Ɗan Majalisar Wakilai ta Ƙasa a Majalisar Tarayya a ƙarƙashin CPC, jam’iyya maras galihu a lokacin. Me ya faru, talakawa da masu halin Ƙananan Hukumomin Gombe/Kwami/Funakaye sun zuba masa ƙuri’un da babu wani Ɗan Majalisa da ya samu kusan yawan ta shi a 2011, kakaf ɗin su har su 360 a Najeriya.

 

Yayin da Mailantarki ya samu ƙuri’u *122,987*, abokin takarar sa na PDP kuwa ƙuri’a 44,206 ya samu. Shi kuma na ANPP ya tashi da ƙuri’un da ba su wuce a jefa cikin aljihun riga malum-malum ba, wato guda 8,760 kacal.

 

Fitar Mailantarki daga APC a cikin watan Mayu, 2022 ke da wuya, sai NNPP ta ba shi takarar gwamna.

 

Alamomin Mailantarki zai firgita manyan namun dajin siyasar Gombe na cikin gwamnati ta fara ne tun daga lokacin da NNPP ta ba shi takara babu hamayya. Wakilai 342 daga Ƙananan Hukumomi 11 duk su ka amince da shi, babu hamayya.

 

Sannan kuma shi da kan sa bayan ya lashe zaɓen fidda-gwanin da wakilai 342 ɗin zu ka zaɓe shi, ya ce, “a tarihin Jihar Gombe ba a taɓa yin zaɓen fidda-gwanin da ya kai na sa zama sahihi ba. Wannan ma alama ce mai nuni da cewa Mailantarki ya samu tagomashi a faɗin jihar kenan.

 

Ko ma dai me ke nan, ganin yadda guguwar Mailantarki ke kwashe manya da ƙananan ‘yan APC da PDP, su na watsi da laima da tsintsiya su na rungumar kwandon kayan marmari, hakan alama ce mai nuna cewa za a kwashi ‘yan kallo a ranar kokawar zaɓen 2023.

 

Tabbas Gwamna Inuwa Yahaya na da aiki a gaban sa. Kuma duk irin inuwar da Inuwa ya shiga da rana, to zai kasance cikin tunanin hasken Mailantarki. Duk cikin duhun da Inuwa Yahaya ya shiga da dare, sai ya yi tunanin hasken Mailantarki. Kai, ko cikin hasken lantarki ko hasken taurari da farin wata Inuwa Yahaya na APC ya shiga, zai ya riƙa tuna hasken Mailantarki.

 

Farin jinin Mailantarki zai iya sakar wa sauran ‘yan takara sukuntumau, ta yadda ko haske fitilar cocila su ka gani, su ce hasken lantarkin Mailantarki ne

 

Wataƙila ma ko a mafarki, ba zai rasa yin mafarkin hasken lantarkin Mailantarki ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce
Manyan Labarai

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

October 4, 2025
Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya
Rahotonni

Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya

October 4, 2025
Bashin Karatun Dalibai: Arewa Maso Yamma Ce Kan Gaba Wajen Cin Gajiyar Shirin
Rahotonni

Bashin Karatun Dalibai: Arewa Maso Yamma Ce Kan Gaba Wajen Cin Gajiyar Shirin

October 3, 2025
Next Post
Umarnin Kotu: Gwamnatin Kano Ta Kulle Masallatai Da Makarantar Abduljabbar Kabara

Umarnin Kotu: Gwamnatin Kano Ta Kulle Masallatai Da Makarantar Abduljabbar Kabara

LABARAI MASU NASABA

Guguwar Ritaya Na Barazana Ga Ayyukan Hukumar Kwastam Yayin Da Jami’ai 825 Za Su Yi Ritaya

Guguwar Ritaya Na Barazana Ga Ayyukan Hukumar Kwastam Yayin Da Jami’ai 825 Za Su Yi Ritaya

October 10, 2025
Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

October 10, 2025
An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi 

An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi 

October 10, 2025
Nijeriya

Haramcin Haƙar Ma’adanai: Majalisa Za Ta Kawo Ƙarshen Asarar Dala Biliyan 9 Duk Shekara

October 10, 2025
Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

October 10, 2025
Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (3)

Yadda Za A Magance Yawaitar Malaman Da Ba Su Cancanta Ba A Nijeriya – TRCN

October 10, 2025
Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

October 10, 2025
Mailantarki

Burin ‘Yan Nijeriya Bai Cika Ba Tun Bayan Samun ‘Yancin Kai

October 10, 2025
Matatar dangote

ACF Ta Yi Zargin Shiri Na Musamman Don Rusa Matatar Man Dangote

October 10, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

October 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.