Ra’ayin Al’umma Akan Dalibin Da Yayi Wa Malamarsa Dukan Kawo Wuka

A wannan makon mun nemi jin ra’ayin al’umma a kan dukan kawo wuka da wani dalibi mai ”Waliyullah” suna na Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara ya yi wa Malamarsa mai suna “Mrs zakariyya”, Malamar ce ke kula da ‘Project’ din na kamala karatu, ana tunanin wani sabai ne ya shiga stakanin su. Ga yadda ra’ayin mutanen da suke tofa albarkacin bakin su ya kaya.

 

Bashir Ibrahim Khalil

Assalamu Alaikum, ag askiya yakamata a dauki  mataki kansa, saboda malami ba abin wasa bane, a nuna masa kuskurensa. Allah ya taimaki malaman mu.

 

Muhd Basheer Sa’ad

Batu na gaskiya babu mutunci a nan! Kuma ya kamata kungiyoyin malamai su dauki mataki a kansa, malami dai malami, don wanda duki malaminsa zai iya dukan mahaifansa.

 

Sunusi Showboy

Ta yaya abin da ya yi zai zama daidai? Koda yake bamu fahimci dalilin da ya janyo har ya yi wannan danyen hukuncin ba.

 

Faty Syaki

Ina fa dai dai anan, Malaminka! to lallai a dauki mataki don wannan ba karamin abu ba ne. Allah ya kyauta.

 

Hassern Mustapha

Ko kadan wannan dalibi bai yi daidai ba, kuma wannan ya nuna tsantsar rashin tarbiyyar da yake dashi, na tabbata idan wani ne ya yi wa mahaifiyarsa ko matarsa haka ba zai taba jin dadi ba. Kuma ya kamata hukumar makarantar ta kore shi, sannan a buga a duka jaridun kasarnan kada wata makaranta ta sake daukarsa. Kuma alkali ya hukuntashi daidai da abinda da ya aikata, hakan zai zama izina ga dukkan wani dalibi da yake kokarin aikata hakan nan gaba.

 

Ibrahim Hassan Baban Adila

Wannan ya nuna bashi da tarbiyya ko kadan, domin malami ko wasa yake koyarmaka, yakamata ka girmamashi ballantana abin da zai amfaka duniya da lahira, don haka ya cancanci hukunci.

 

Ummul Banaat

Waliyullah be kyauta ba koma wane irin abu tamasa bai kamata ya daketaba matsayinta na malamarsa, duk da de wasu ‘project superbisors’ akwai rashin mutunci, musamman ma mata, ayi ta wulakantaka a kan abu kalilan, amma da ya danne zuciyarsa tunda komai ya zo karshe, amma kaddara ta riga fata, yanzu ya barnatar da shekara 4 zuwa 5 a banza.

 

Mariya MD Abdurrahman

Ya yi daidai tunda basu da kirki a kan ‘Project’ sai su rike mutum sama da shekara 5 ba tare da wani daliliba, irin wadannan Malaman Allah ya hada su da wanda ya fi haka.

 

Abdussalam Nasir Lalan

Idan bera da sata, daddawa ma da wari.

 

Jameela Bajee

Gaskiya bai yi daidai ba, koma menene ta yi masa, ya dauki irin wannan mummunan mataki, Allah ya shirya mana zuri’a.

 

Sulaiman Lawal Abdullah

Ni dai a tunanina bai yi daidai ba, duk da cewa wadansu malaman su suke hasala dalibai har ayi musu rashin kunya, wani malamin don kana dalibi kwata kwata basa girmama alakarsu da mutunta dalibai.

 

Maryam Nuhu Turau

Tsabar Iskanci ne da wulakanta Malamai da aikin koyarwa, ya kamata a hukunta shi ta hanyar korarshi daga makarantar tare da hana shi ‘Admission’ a duk fadin makarantun Nijeriya, wannan zai zama darasi ga ‘yan baya.

 

Mahdee Bashir

Toh ai gashi ya ga sharrin zuciya, da ya mika wa Allah lamarinsa da abin yazo da sauki.

 

Aleeyu Yusup Gusau

Abu na farko da za a tambaya a nan shine me yasa ya dake ta? Saboda haka kawai ba zai sameta ya daketa ba ba tare da wani dalili ba, amma kuma ko akwai wani dalilin hakan ba zai bashi damar dukan malamarsa ba, hasalima kuma matar aure a nan ya yi kuskure babban koda kuwa ta yi laifi.Yanzu dukan da ya yi mata to duk ya wanke laifin da ta yi masa, shi ne babban mai laifi dole ne hukumar makaranta ta dauki tsatssauran mataki akansa ta yadda gobe wani dalibi ba zai daki malami ko malama ba.

 

Adam Suleiman

Gaskiya bai dace ba ko kadan, wannan ai rashin tarbiya ce.

 

Jamila Seyoji

A zahirin gaskiya wannan dalibi bashi da ta ido, amma ina kyautata zaton illar kwaya ne, domin ita kwaya masana sun bayyana cewa duk mai ta’ammali da ita tofa babu abinda ba zai iya aikata wa ba. Allah ya shirya.

 

Adamu Yunusa Ibrahim

Wannan yana nuna har yanzu matasan Nijeriya ba su san inda suka dosa ba. A yadda labarin ya zo ya nuna cewa matashin ne ya yi tafiya zuwa Legas ya ziyarci abokinsa, sai aka samu akasi ‘yansanda suka kama shi suka tsare har tsawon wata biyu. Bayan ya kubuta ne ya ankara cewa bai yi wani aikin kwarewa da ake tura dalibai mai suna SIWES, shi ne ya je wajen malamar da nufin kawai ta tsallakar da shi cewa ya yi wancan aikin. Ita kuma ta ce hakan cin amana ne, sai dai ya dawo wata shekarar ya cika ka’ida. Bata yi aune ba ya fara jibgarta, da bakinsa ya fada cewa bata yi yunkurin ramawa ba, amma ya ci gaba da dukanta har ta kai kasa.

Ra’ayina shi ne hukuncin da hukumar makarantar ta dauka na korar wannan dalibi mai saurin hannu ya yi dai-dai. Domin ana bayar da shaidar Digiri ne ba kawai dan ka ci dukkan darusan da aka koya maka ba, har da Tarbiyya da Da’a da Yakana da sanin girman nagaba da kai. Allah ya kare mu daga sharrin irin wadannan Daliban.

 

Fiddausi Abubakar

Zancen Gaskiya wannan dalibi bai kyauta ba komai idan aka sa hakuri a ciki yafi, sannan suma malamai ya kamata su rinka adalchi wa dalibansu don Allah ya baka dama irin wannan bai kamata kana wulakanta mutane ba. Gaskiya wasu malamai kam saika kai zuciyarka nesa akansu idan ba haka ba zaka iya musu komai.

 

Abdullahi Isah Kmaiyaki

Mu daliban Jami’ar Gwamnatin Tarayya Dutse muna Allah wadai ga wannan dalibi kuma abin da ya yi sam bai kyauta ba ko mai ta yi masa, ai malamarsa ce.

 

Zee Waziri

Gaskiya bai yi daidai ba, sannan kuma ai shi ya ja wa kansa saboda shi ne bai yi IT ba, sannan duk abinda ta yi masa bai kamata ya dake ta, ai akwai hukumar makaranta dai sai ya kai karanta a can idan yana da gaskiya za su goyi banyan sa.

Exit mobile version