ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, June 14, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ra’ayin Matasa Game Da Auren Kusa Da Na Nesa

by Rabi'at Sidi Bala
2 months ago

Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zaƙulo muku batutuwa daban-daban waɗanda suka shafi al’umma, ciki sun haɗar da zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.

Tsokacinmu na yau zai yi duba game da abin da ya shafi auren kusa da kuma auren nesa. Akwai samari da ƴanmata waɗanda basu fiya son aure a kusa da su ba, wasu samarin ma garin suke bari gaba ɗaya su nemo aure.

Dalilin hakan ya sa shafin TASKIRA jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; “Ko a ina matsalar take?, laifin waye tsakanin samari da ƴan mata?, ko akwai wata matsala da auren kusa yake da shi?. Mene ne ra’ayinku game da auren kusa da gida ko unguwa ɗaya ko kuma gari ɗaya?”.

ADVERTISEMENT
  • Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi
  • Gwamnati Ba Za Ta Saki ’Yan Ta’adda Ba Duk Da Kisan Tsohon Kakakin DHQ — Tinubu
  • Yadda Ake Wainar Masara Da Miyar Yaji
  • Hanyoyin Hada Humra Mai Kamshi
  • Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (1)

Ga dai bayanan nasu kamar haka:

Sunana Comr, Nr.Ibrahim Lawan Stk:

LABARAI MASU NASABA

Gwamnati Ba Za Ta Saki ’Yan Ta’adda Ba Duk Da Kisan Tsohon Kakakin DHQ — Tinubu

Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF

A gaskiya matsalar tana fitowa daga ɓangarori biyu; wasu samari suna gujewa surutu da tsoma bakin jama’a, ya yin da wasu ƴan mata ke da zaɓi mai tsauri. Amma ba za a ce auren kusa yana da matsala kai tsaye ba, sai dai yadda ake tafiyar da shi, A ra’ayina, auren kusa yana da fa’ida sosai yana ƙara kusanci, fahimtar juna da taimakon iyali. Sai dai yana buƙatar hankali da kiyaye iyaka don kauce wa matsaloli, Shawara ga matasa ita ce kada ku mai da nesa ko kusa a matsayin mizani, ku fi mayar da hankali kan halaye nagari da addini. Inda aka samu nagarta, nan ne mafi alheri.

Sunana Ƙueen-Nasmah daga Jihar Zamfara:

Matsalar auren kusa a ɓangaren mace, shi namijin kan iya yin duk abin da ya ga dama dan ganin ai ana tare, amma a nesa an yin abin baƙunci dan ganin ai ita baƙuwa ce, cin kashin da za a yi ma ta kusa, ta nesa ba za a yi mata ba. Nawa ra’ayin kuwa game da hakan ba komai bane face mutum yana so ya samu ci gaba, aƙalla idan har ka yi auren nesa za ka ƙara samun gogewa ta bakin abubuwa da ba ka da su. Shawarata game da auren kusa ko nesa ba komai ba ne face kar ku matsanta dole sai nesa ko sai kusa, domin yin hakan na iya sa ka gujewa alkhairinka, ƙila kai ta kusan ita ce alkhairinka, kai kuma ƙila ta nesa ce taka alkhairin, aure dai sunansa alkhairi, mafi alkhairin shi ne a zauna lafiya.

Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rano, A Jihar Kano:

Laifin na duka biyun ne gaskiya, domin mafiya yawan samari da ƴan matan yanzu ƙarya tafi yawa to, kuka ana zaune waje guda kowa ya san kowa. Yana da kyau kuma yana ƙara danƙon zumunci kuma yafi sauƙin kashe kuɗi duba da yanayin wannan rayuwar. Yana da kyau yin auren kusa da gida da kuma ƙara tsarkake zuƙata da janyo kyakkyawar mu’amala a tsakanin juna sannan ayi shi saboda Allah.

Sunana Sunusi Ibrahim sml.:

Raini ne zai shiga tsakaninku musamman ta sanka sosai har gida. ba ya birge da yawan matasa, saboda halin ƴan matan sai haƙuri. shi ne kowa ya so auren nesa saboda duk karatun daka koya mata shi za ta ɗauka, dalilin ta san ba tada kowa sai kai, kai za ka zamo madubi gare ta.

Sunana Yusuf M. Bawa Maƙarfi Road, Rigasa Kaduna:

Mukan guji auren kusa  saboda ƙalubalen ƙawaye da kuma dangin amarya.. Ko da ƴan unguwa ɗaya sun yi aure to, kar su zauna a kusa da unguwar da suke, su chanza unguwa. Ku yi aurenku a kusa amma kusan inda za ku zauna nesa da gidanku na da.

Sunana Zainab Zeey Ilyas, Jihar Kaduna:

Ni ra’ayina ba na son gaskiya auren kusa, na fi son auren nesa, saboda sai ya fi ƙarko. Idan ka auri namijin da ya sanka a unguwa tun ƙuruciya ai akwai matsala, amma wanda yake nesa bai sonka ba balle wataran ya goranta maka, ko ya gwaɓa maka magana, ko danginsa su riƙa cin mutuncinka ko na gidanku. Kuma idan ka auri na nesa ko ba komai kun ƙaro sabbin dangi a gidanku, ba waɗanda ku ka saba gani ba. Ni gaskiya ko namijin da zai zauna a kusa da gidansu ba so nake yi ba, na fi son wanda ban san shi ba, bai sanni ba, inda za mu zauna ma mu je musu matsayin baƙi, kin ga mutum ya sake sabuwar rayuwa ya bar ta ƙuruciya gabadaya.

Sunana Abdul Rahaman Muhammad Sani, Gashu’a, Bade LGA, Jihar Yobe:

Matsalar tana da sarƙaƙiya, laifin na samari ne da ƴan mata. Wasu samari sun fi son auren ƴan mata na nesa, wasu ƴan mata ma sun fi son auren samari na nesa. Auren kusa da gida ko unguwa ɗaya yana da matsala, domin yana iya haifar da gabatarwa da kuma gabatar da hankali. Auren kusa da gida ko unguwa ɗaya yana da kyau, domin yana sa a samun taimako da kuma kuwa da hankali. Amma yana da muhimmanci a duba da kyau kafin a yi auren, domin auren kusa da gida ko unguwa ɗaya yana iya haifar da matsala. Shawara ga matasa, Auren kusa da gida ko unguwa ɗaya yana da kyau, amma a duba da kyau kafin a yi auren. Auren na nesa yana da kyau, amma a duba da kyau kafin a yi auren.Yana da muhimmanci a nemi ilimi da kuma kuwa da akali kafin a yi auren.

Sunana Yakubu Gwammaja:

Auren kusa ko nesa rabo ne ko ince ƙaddara ne, duk inda matarka take sai ka je ka Nemota. idan har na sami mata mai hankali ko da gidan mu ɗaya zan iya auranta mu zauna lafiya. idan har baka da kuɗi gaskiya ka sami mai hankali ka aura, saboda tsadar rayuwa.

Sunana Samaila Muhammad MGN:

Kowa yana da laifi amma samari suna gani hakan yana jawo gutsiri tsoma. mace tana ganin tare kuka taso ta san komai naka ba dole ku sami jituwa ba. Shawara ba wai ba a son auren na kusa bane, amma wani zuɓin idan aka ɗan matsa za a sami sauƙi.

Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    GORON JUMA’A
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ban Sha Wata Wahala Ba A Gwagwarmayar Shiga Harkar Fim —Hadiza

MASU ALAKA

Gwamnati Ba Za Ta Saki ’Yan Ta’adda Ba Duk Da Kisan Tsohon Kakakin DHQ — Tinubu
Manyan Labarai

Gwamnati Ba Za Ta Saki ’Yan Ta’adda Ba Duk Da Kisan Tsohon Kakakin DHQ — Tinubu

June 14, 2026
Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF
Rahotonni

Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF

June 13, 2026
Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin
Rahotonni

Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin

June 13, 2026
Next Post
Al’umma Sun Ƙi Amincewa Da Shirin Gwamnatin Ogun Na Mayar Da Makarantu Ga Ƴan Misham

Al’umma Sun Ƙi Amincewa Da Shirin Gwamnatin Ogun Na Mayar Da Makarantu Ga Ƴan Misham

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi

Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi

June 14, 2026
Gwamnati Ba Za Ta Saki ’Yan Ta’adda Ba Duk Da Kisan Tsohon Kakakin DHQ — Tinubu

Gwamnati Ba Za Ta Saki ’Yan Ta’adda Ba Duk Da Kisan Tsohon Kakakin DHQ — Tinubu

June 14, 2026
Yadda Ake Wainar Masara Da Miyar Yaji

Yadda Ake Wainar Masara Da Miyar Yaji

June 14, 2026
Hanyoyin Hada Humra Mai Kamshi

Hanyoyin Hada Humra Mai Kamshi

June 14, 2026
Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (1)

Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (1)

June 13, 2026
Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF

Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF

June 13, 2026
Muhallin Halittu Da Aka Yi Gado A Kasar Sin Sun Samu Ci Gaba Ta Fuskar Ba Su Kariya

Muhallin Halittu Da Aka Yi Gado A Kasar Sin Sun Samu Ci Gaba Ta Fuskar Ba Su Kariya

June 13, 2026
Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin

Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin

June 13, 2026
Sake Jan Damarar Soja Da Japan Ke Yi Karin Alama Ce Mai Hadari

Sake Jan Damarar Soja Da Japan Ke Yi Karin Alama Ce Mai Hadari

June 14, 2026
NANS Ta Kafa Kwamitin Ganin Yadda Ake Tafiyar Da Ayyukan TETFund

NANS Ta Kafa Kwamitin Ganin Yadda Ake Tafiyar Da Ayyukan TETFund

June 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.