A mafi yawancin lokuta, masu sha’awar kallon fina-finai, kan dauki jaruman masana’antar shirya fina-finai a matsayin mugaye, ‘yan iska ko kuma marasa mutunci, hakan bai rasa nasaba da irin role din da jaruman kan fito a cikin fina-finan da suke dauka ba.
Manyan jarumai, musamman mata a masana’antar Kannywood da suka hada da marigayiya Saratu Gidado, Hauwa Waraka da sauran jaruman da suka taka rawa a wancan lokacin, sun fuskanci abin da za a iya kira a matsayin kalubale kwarai da gaske.
Daga Baba Lami a cikin shirin GARWASHI, zuwa Kilishi a cikin LABARINA da kuma sauran wadanda kan fuskanci kyama ko a wani lokacin ma har da barazana, daga wadansu da ke kallon abin da suka yi a cikin fina-finan da abin da bai dace ba, a kwanakin baya, Baba Lami kamar yadda aka fi saninta ta bayyana cewa; mutane da dama na yi mata kallon kamar wata mara imani da tausayi, duba da irin rawar da ta taka a cikin shirin fim mai dogon zango, wanda kamfanin UK Entertainment suka shirya.
Ta yi ikirarin cewa, a wasu lokutan tana tsoron fita waje ita kadai, saboda abin da za ta iya fuskanta a wajen wasu, musamman matasan da ke ganin ta yi ruwa ta yi tsaki, wajen hana Ma’u rawar gaban hantsi a gidan mahaifinta a cikin shirin, har takai ga ta rasa nutsuwa a daidai lokacin da ya kamata a ce ta huta, duba da yawan shekarunta a duniya.
Haka abin yake a bangaren Hauwa Farar Lema, wadda aka fi sani da Kilishi, sakamakon rawar da ta taka a cikin shirin fim mai dogon zango na LABARINA da kamfanin Saira Mobies suka shirya, a cikin shirin an hango Kilishi tana shiga rayuwar wani Yarima a wata babbar masarauta, har ta kai ga kokarin hana shi auren wata yarinya ‘yar talakawa da yake so, inda ta bayar da hujjar cewa; bai kamata a ce yaron gidan sarauta kamar shi ya auri yarinyar da ta taso a gidan talakawa ba.
Duk da cewa an yi auren, amma Kilishi ta kasa boye irin kiyayyar da take yi wa matar ta hanyar kulla mata sharri kala-kala, har ta kai ga ta zargi amaryar Yariman da kashe wata ‘yar gidan sarauta, bayan kuma kokarin kawar da yaron da ma’auratan biyu suka haifa daga duniya da ta yi, hakan ba karamin jawo mata fushin al’umma ya yi ba, duk da cewa; shirin fim ne, amma hakan bai hana wasu mutane nuna mata fushinsu a fili ba.
A wata hira da ta yi da jarumar Kannywood Hadiza Aliyu Gabon, a cikin shirinta na Gabon’s Room Talk Show, Hauwa Farar Lema, ta bayyana cewa; rol din Kilishi da ta yi a cikin Labarina, ya jawo mata daukaka matuka, domin kuwa a dalilinsa ta ce ta taka inda ba ta taba tsammanin takawa ba, amma kuma a daya bangaren ya jawo har wasu sun yi mata rauni a hannunta, inda suka bayyana cewa; babu abin da zai hana su daukar wa Sumayya wadda ita ce matar Yarima Raba Gardama, fansa a kan ita Kilishin da ta hana su jin dadin aurensu ba.
Hauwa ta ce, “Wata rana, ina cikin Adaidaita Sahu sai aka kira ni ta waya, sai na cire Takunkumin fuskata (Face Mask), domin daukar kiran, hakan ya sa wasu matasa suka gane ni ce a wajen, sai suka fara zage-zage suna cewa, dole ne su daukar wa Sumayya fansa a kaina, tunda na hana su jin dadin aurensu ita da mijinta Yarima”, da farko mutum daya ne ya gane ni, amma cikin lokaci sai ga wasu mutum hudu sun fito cikin fushi suna zage-zage kamar yadda na farkon yake yi.
Ta ci gaba da cewa, “Wanda yake janye da Adaidaita Sahun da nake ciki, sai ya tambaye su abin da na yi musu, nan da nan suka yi kansa, suna kokarin cutar da shi, ganin haka ya sa na yi kokarin hana su, wanda har ya jawo suka yi min rauni a hannuna” inji Hauwa Farar Lema, kuma Kilishi a cikin shirin Labarina.
Kilishi ta ce, ya kamata mutane su gane cewa; babu yadda za a yi shirin fim ya burge su, matukar babu bata gari a cikin jaruman da za su fito a cikinsa.
A bangaren jarumai maza kuwa, akwai irin su Tanimu Akawu, Alasan Kwalle da Rabiu Rikadawa, wadanda su ma a wasu lokutan kan fito a matsayin wadanda ba su bai wa kudi kunya, ko da kuwa a ce an yi rashin sa’a kudin na haramun ne.
Tanimu Akawu, ya taba bayyanawa a wata hira da ya yi cewa; sau da dama, ya kan tambayi masu bayar da umarni a cikin fim cewa, mene ne ya jawo ake saka shi a matsayin wani mutumin kawai a mafi yawan fina-finansa, amma amsar da yake samu ita ce; wannan bangaren ya fi dacewa da shi, duk da cewa a zahiri mutum ne mai saukin kai da gudun duniya.
Hakan ya sha faruwa ga jaruman fina-finai a fadin Nijeriya, inda suke fuskantar musgunawa da barazana, sakamakon wani rol da suke takawa a cikin fina-finan, wanda bai yi wa wasu dadi ba, amma kuma a mafi yawan lokutan, jarumai mata sun fi fuskantar hakan, ba abu ne mai sauki a wajen wasu su yarda cewa; shirin fim ba da gaske ba ne, saboda a wasu lokutan a kan samu wasu da za su dinga sharbar kuka a yayin da suke kallon fim, sakamakon wani jarumin da suke tausayawa a cikin shirin da suke kalla.
Irin wadannan role da jarumai ke takawa a cikin fina-finai na jawo musu dimbin masoya da kuma akasin haka, yayin da za ka ji wani ya ce, yana sha’awar jarumin da ba ya daukar raini a cikin fim, wani kuma sai ya ce; ya fi sha’war jarumi mai sanyin hali da tausayawa, idan an yi masa kuskure a cikin fim, koma dai mene ne, bai kamata a ce jaruman da ake dokin gani sun fito a wasu sabbin fina-finai masu ilimantarwa da nishadantarwa kuma a buge da yi musu illa ba.














