Ibrahim Sodangi fitaccen Jarumi ne a masana’antar Kannywood kuma an san shi dama, ta hanyar Film, musamman a Arewacin Nijeriya, ya kuma fito a cikin Fina-Finan hausa da dama.
A hirarsa da waklinmu na Kaduna ABUBAKAR ABBA, Sodangi ya zayyano wasu daga cikin Fina-Finan da ya fito, musamman yadda ya fara haɗuwa da fitaccen Jarumi, Adamu Zango.
Tarihin Rayuwa:
An haife ni a, jihar Kaduna, na fara yin karatu, a makarantar firamare ta Army da ke a NDA kaduna, daga nan, na wuce makarantar sakandare ta gwamnati da ke a Kurmin Mashi Kaduna, a kwana a tashi, a tashi, sai na tsinci kaina, a masana’antar Kannywood.
Shekarar Da Na Shiga Masana’antar:
Na shiga masana’antar, a 2014, ba zan iya mantawa ba, akwai wasu kamfanonin yin wasan Dirama da suke yin rihasal ɗin a cikin garin Kaduna, a wata Cinema, ni dama na kan je ne, domin Allah ya bani basira na iya rubutu da karatu.
Ina zuwa gurin a kwana a tashi, sai ya zamanto, idan masu shirin yin Diramar suka bayar da takardar da ke ɗauke da tsarin wata Dirma da za su yi, a wajen, sai masu kamfanin su rinƙa buƙatar waye zai iya karanta takardar, ni kuma a lokacin, ina kallon su, sai nag a, ah!! to ai ni ma, zan iya karanatawa.
Sau da yawa, su burinsu, su ga sun fito a cikin Film ɗin, tunda su ne, suke yin acting ɗin.
Sai na amshi takardar, na ce masu bari in ɗan karanta, akwai wani an ace masa Darakta, kuma shi, bai sannni ba kuma ban taɓa, ganinsa ba, sai ya tambaya cewa, wancan wanene, wato ni ke nan, to shi asalin mai kamfanin, sai ya cewa Daraktan ai ya sanni, tunda a unguwar su nake.
Sai suka bani takardun, na karanta masu, a Dimar da za su yi, kai tsaye, na gama karantawa, sai ya ce, don Allah in rinƙa leƙowa wajen da suke yin rihasal ɗin mana, sai na ci gaba da leƙawa, ina ci gaba da ganin abuwan da suke yi.
Daga nan, sai ya haɗa ni da Adamu Zango, kasan ladabi da biyya, su ne ke kai mutum wani matsayi, na ci gaban rayuwarsa. Yau da gobe, sai na gano ashe Adamu Zango na da ofis a Magadushu a Kaduna, a wancan lokacin, akwai wani ƙaninsa Kabiru, Rabi’u, Shua’ibu, suna dai da yawa, sai na ce, shi kenan, na yi abokai a nan ke nan.
A hankali- a hankali, sai na shiga ran Adamu Zango, sai ta kasance, kullum ina shiga cikin studio ɗinsa, akwai wara rana, Adamu Zango ya ce min Sodangi, za a je wani wani shooting film, mai suna Kambun So, shi ne film ɗin farko, da na fara anya ni, a ciki, wanda na fito sau ɗaya, a cikinsa.
Rawar Da Na Taka A Film Ɗin Rumbun So:
Na fito ne, a cikin Daji, ma’ana, masu tare mutane suna ƙwace abinda ke hannunsu, ana nan, ana nan, aka gama wannan Film ɗin, aka tashi, da yawa wanda muka je da su gun, suka ce, kayi ƙoƙari suka tambaye ni, daman a taɓa yin Film ne? na ce ma su ban taɓa yi ba, wannan shi ne, karo na farko.
Yau da gobe, yau da gobe, sai su kira ni, na yi Film, da yaw aba adadi, idan na ce zan jero maka sunayen Fim da na fito, kuma suka suka yi shura, sai mu kai Magariba a nan.
Film Ɗin Baya-Bayan Nan Da Na Fito Wanda Ya Yi Shura:
Gaskiya, akwai Film ɗin Babban Yaro, na Adamu Zango, akwai na Mamajo, akwai na Karan Bana, akwai na Soyayyar Facebook. Har gobe, Fim ɗin da ina kallonsa, a Idanu na, shi ne, na Babban Yaro, ko yanzu aka nuna shi, sai inga kamar yau aka yi shi.
Fim ɗin ya kai maƙura, domin ya ɗauki hankalin masu kallo da yawa, ya isar da saƙo a fanni da ban da ban.
Rawar Da Na Taka A Film Ɗin Na Manajo:
Akiwai kuma Fim cin na Manajo, ka ga Film ɗin, duk abuwan da aka yi a cikin shi, wallahi, a yazu zai yi wuya, a sake yinsu.
Na fit ne cewar ni, ina da budurwata, ina cewa akwai ta wajen yin saye-sayen kaya wato shopping, ina kashe mata kuɗaɗe, ina yi mata duk abinda ranta yake so. Sai na zamanto, ana gurin ana yin kasuwanci, akwai chairman Alh. Rabilu Musa Ibro, shi ma ma’aikaci ne a bakin Gate ɗin ƙofar Gate ɗin, akwai kuma Adamu Zango da Haruna, suma suna yin aiki, a bakin Gate ɗin,
Kasan al’adar mai gadi, idan kana yi masa alheri, domin idan na zo, na kan ɗauki kuɗi ina ba su, sai suka rinƙa kira na da Babban Yaro.
Rawar Da Na Taka A Film Ɗi Na Soyayyar Facebook:
Na fito a matsayin abokin Jarumin Film ɗin, wanda ke neman Jarumar Film ɗin, ina ba shi shawarwari, ina ɗora shi a hanya cewar, tana ƙaunarsa, kar ya ci amanarta, sai ya zamanto mutane da yawa, sun so ni. Ni kai na, ya ƙayatar da ni.
Sana’ar Film, ita ce muka sani, mutane sun sanmu, mun kuma samu alkhairai da yawa, kuma duk wand aka ga ya yi shura, a sana’ar a yanzu, ko dai ya da sharafi, ko kuma Allah ya kafa shi, idan ka ce masa, Ibrahim Sodangi, ya sanni, saboda mun yi zaman na amana da yawa, kamar dai irisu Na Bursuka, wanda yana daga cikin masu gida na, a masana’antar, muna koyon abubuwa da yawa, a gunsu, sukan zaunar da mu, su bamu shawarwari, kan sana’ar.













