ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Al’umma Sun Ƙi Amincewa Da Shirin Gwamnatin Ogun Na Mayar Da Makarantu Ga Ƴan Misham

by Sani Anwar
5 months ago

Ƙungiyar Limamai da a Jihar Ogun, ta yi watsi da shirin Gwamna Dapo Abiodun, na mayar da makarantun gwamnati ga ƙungiyoyin ƴan mishan, inda ta bayyana matakin a matsayin “abu maras kyawu da tsokana da kuma rashin gaskiya.”

Daily trust ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne, Abiodun ya bayyana shirin gwamnatinsa na mayar da makarantun mishan a jihar ga iyayensu na asali a wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa haɗin gwiwa a ɓangaren ilimi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne, a ranar Juma’a a lokacin da yake karɓar baƙuncin limamin coci a Nijeriya, Archbishop Michael Francis Crotty, a wata ziyarar ban girma da ya kai ofishinsa da ke Oke-Mosan, Abeokuta.

ADVERTISEMENT

Wakilin ya samu rakiyar Bishop ɗin Katolika na Ijebu-Ode, Francis Obafemi Adesina, Bishop na Abeokuta, Peter Odetoyinbo da sauran jami’an cocin.

“Za mu mayar da dukkan makarantun mishan ga masu su. Muna buƙatar mu haɗa hannu da mutane masu zaman kansu, sannan kuma mu ƙarfafa haɗin gwiwa tare da Coci, domin faɗaɗa ci gaba,” in ji gwamnan.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Litinin, Imam Tajudeen Mustafa Adewunmi, babban sakataren ƙungiyar limamai da Alfas ta Jihar Ogun, ƙungiyar ta yi watsi da shirin, inda ta bayyana shi a matsayin wanda ya saɓa wa ƙa’idojin daidaito.

“Wannan manufar, ba kawai babban kuskure ba ne a tarihin ilimin jihar, har ma da cin zarafi tare da haɗari ga ƙa’idodin daidaito, adalci da daidaiton addini a cikin jama’a,” in ji ƙungiyar.

A cewar Limaman, makarantun gwamnati a Jihar Ogun, na kowa da kowa ne, “don haka, akwai buƙatar kawar da irin salon mulkin da da gwamnati ke son dawo da shi yanzu.”

Adewunmi ya gabatar da cewa, “Bari a bayyana wannan tsari ba tare da wata shubuha ba: Wannan matakin na nuna wariya ne gaba-ɗaya, wanda ba za a amince da ita ba kwata-kwata, domin hakan yana nuna a shirye gwamnati take wajen fifita muradun wata ƙungiya ta addini a kan wata.

“Al’ummar Musulmi, waɗanda suka kasance yanki mai ɗimbin yawa da tarihi na Jihar Ogun, ba za su tsaya a yayin da ake shirin yin watsi da ƴancinsu da hankalinsu da kuma gudummawar da suke bayarwa ba, ba za mu yarda da duk wata manufa da take neman a mayar da cibiyoyin gwamnatin da aka gina aka kuma inganta su zuwa ga tsarin ɓangaranci a ƙarƙashin kowace irin fuska ba.”

Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Next Post
Akwai Yiwuwar Sake Tsare Ni Dindindin – El-Rufa’i

Akwai Yiwuwar Sake Tsare Ni Dindindin - El-Rufa'i

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.