A ranar Talata 1 ga watan Oktoba Nijeriya ta yi bikin cika shekara 64 da samun mulkin kai daga Turawa. Wasu ‘yan Nijeriya sun bayyana yadda suke ji da kuma fatan da suke da shi a kan wannan biki. Yayin da wasu ke cewa Nijeriya ta cikia burin a daidai wannan lokaci wasu kuma na ganin samsam Nijeriya bata yi abin azo a gani ba musamman in aka lura da wasu kasashe tsasrarrakin kasar nan, wadanda muka samu ‘yancin kai a kusan lokaci daya amma sun yi mana wajen ci gaba da bunkasar tattalin arziki ga dai yadda suka bayyana ra’ayoyin na su.
Alh. Adamu Muhammed Makarfi: Mai fashin baki a al’amuran yau da kullum. A nawa ra’ayin, koda ma gwamnatin ta bayyana cewa, ba za ta gudanar da shagulgulan bikin zagayowar ranar ta samun ‘yancin kan Nijeriya ba, koma za ta yi dai, akasarin ‘yan kasar musamman talakawa da bas u iya ciyar da iyalansu sau uku a rana, babu wani da zai damu da wani maganar zagoyowar ranar.
- Wakilin Sin Ya Bukaci Sassan Somaliya Da Su Kara Azamar Warware Sabani Ta Hanyar Tattaunawa
- Habasha Ta Jinjinawa Masu Zuba Jari Na Kasar Sin
Tun daga badi zuwa yau, da gwamnatin ta hau karagar mulkin kasar, babu wani abu da sauya na ci gaba, illama ma dai, sai kara jefa akasarin ‘yan kasar da gwamnatin ta yi a cikin ukubar rayuwa, musamman ta hanyar cire tallafin man fetur da ta yi.
Irin wadannan tsauraran tsare-tsaren da gwamnatin ta zo da su, sun kara tagyyar rayuwar talakawan kasar.
Hajiya Aisha Abubakar :Shugabar gidauniyar Zulifata da ke a jihar Kaduna da ke sasanta ma’aurata da kwatowa kananan yara hakkinsu, ta ce, a kullum kwannan duniya a gidauniyra mu, muna karbar korafe korafe iri-iri daga gun mata kan yadda mazajensu ke gaza ciyar da iyalansu, duk wannan zan iya cewa, ya samu asali ne daga irin tsararan tsare-tsaren da gwamnatin ta zo da su, musamman kara farashin man feutr da kuma cire tallafin mai.
Ta ce, karain abun takaici shi ne, yadda wasu magindantan ke bin dare, suna shiga cikin gonakai domin satar kayan amfanin gona da manoma suka girbe domin su ciyar da iyalansu.
Yau ko da magidanci dan kasuwa ne, ko da yaje kasuwar, babu wani gwabbaban ciniki da zai yi da zai iya kula da rayuwar iyalansa.
Malam Zakari Adamu: Shi kuwa wani malami a kwaleji kimiyya da fasaha ta tarayya da ke a Jihar Kaduna Malam Zakari Adamu ya ce, a nasa ra’ayin har yanzu gwamnatin da lamau ba ta dauki hanyar samarwa da ‘yan kasar sauki ba domin kuwa, a kullum tunaninta, kara karkata yake a kan jefa ‘yan kasar a cikin kunci ta hanyar fito da tsare-tsare, ba tare da daukar kwararran matakan da za su samarwa da ‘yan Nijeriya sauki ba.
Ya zama wajibi, gwamnatin ta sani cewa, zabar ta aka yi kuma ba mulkin karfa-karfa ya dace ta rinka yiwa ‘yan kasar ba, musamman talakawa.
Malam Babbangida Yola; tabbas shekara 64 a cikin shekarun kasa ba abin wasa ba ne. Nijeriya ta fuskanci gwagwamarwa mai karfi a cikin wadannan shekarun. Tun daga yakin basasa da gano man fetur da bunkasar tattalin arziki a fannoni da dama. Dole a yaba da wadannan ci gaba, amma kuma in aka lura irin ci gaba da aka samu wasu kasashen da muka samu ‘yancin kai a daidai lokaci daya, sai muce abin bai kai yadda ake bukata ba. Matsalar a Nijeriya shi ne yadda shugabanin suna kasa tsayuwa su yi aiki yadda ya kamata da kuma yadda shugabannin bas a son ci gaba da ayyukan da wadanda sduka gaba suka fara na ci gaba.