A yau mun kawo muku ra’ayoyin al’umma a kan hanyoyin fuskantar wannan lokaci na Hunturu, musamman yadda za a kare yara daga matsalolin da ke tattare da sanyin Hunturu da hanyoyin da ya kamata abi wajen ganin an kiyaye yawaitar tashin wuta (gobara) a irin wanna yanayi, ga dai ra’ayoyin maku.
Comr Isma’il Ibrahim Gusau
Wannan lokaci ne da ya kamata iyaye su kula da lafiyar’yan’yan su, domin basu kariya ga kamuwa da cutukan da sanyi ke haifar wa ga yaran su, kamar irinsu sanyin jiki da mura, da Sickler, Nemonear, da sauran su, a rinka sanya masu kayan sanyi, da hanasu wasa ruwa, a rinka yi masu wanka da ruwan zafi.
Fannin yawan goba, yakamata iyaye mata su kiyaye musamman masu amfani da Gas, saboda yawan gobarar da ke faruwa yanzu sakaci idan kaji musabbabin faruwar ta zaka ga sakaci ne ya haifar da ita, a kula da aiken yara kitchen, saboda gudun matsala, a rinka ajiye Gas wurin daya dace.
Amb Ibrahim Adam Dan-Sarauta
Madallah da wannan maudu’i. Sannu da himma Hajiya Aunty Aysher Seyoji, Gare ku iyaye musamman Mata da suke zaune tare da yaransu a gidaje a kowane lokaci. Yanayi na lokacin Hunturu yanayi ne mai wahalar sha’ani ga manya ma balle kananan yara. Idan aka ce an shiga yanayin na Hunturu to za ki ga tsafta ta yi karanci musamman idan aka ce miki ana bukatar a taba ruwane a lokacin tsaftacewar. Ba ma kamar ga kananan yara.
A wannan lokacin ne cututtuka suke shiga saboda ba’a kula da yanayin tsaftar yaran, wanda Babba ma za ki ga da yawa a cikin mutane sai sun dunduma ruwan zafi sannan za su iya yin wanka da shi saboda gujewa matsalar kamuwa da cuta musamman irin ta sanyi, to su kuma iyaye mata ba kowace ba ce take iya dunduma ruwan don yi wa yaranta wanka. Sannan kuma yawan amfani da ruwan sanyi a cikin yanayi na hunturu yana iya yi wa lafiya barazana da haifar da sauran cututtuka a cikin jiki.
Da fatan za mu kiyaye, don kulawa da lafiyarmu. Allah ya sa mu ga wucewa sa lafiya amin.
Faty Syaki
Wannan gaskiane, abinda zance game da yara .ke uwa ki kasance me tattalin yaranki ba kusaki yara sanyi safiya su hallara waje ko makotaba kamasu da safe ki musu wanka wannan wankan safen yana kore sanyi shafa musu mai a tafukan kafafunsa kisanya musu safa, ya zamakansu da hulunan sanyi ya rufe musu har kunnuwansu banda sa garwashi a daki wai don jin dumi wannan babban hatsari ne, wani lokaci gobaran ba zaka san ta inda ta tasoba sai dai nace Allah ya tsare dukacin al’umma baki daya. Allah ya sa mufita sanyin lafiya.
Abdul’aziz Mohammed
Tabbas haka ne, abu mafi muhimmanci da ya kamata iyaye su yi musamman ga yara shi ne su tabbatar daga karfe 5-6 an sanyawa yara kayan sanyi tare da da kauracewa yi wa yara wanka da ruwan sanyi.
Abdul’aziz Mohammed
A baiwa yara kula na musamman kamar kaurace wanka da ruwan sanyi. A tabbatar yayin da aka musu wanka an sanya tufafi da zai taimaka musu domin jin dumi_dumi a tare da su.
Nuruddeen Muhammad Funtua
A gaskiya ya kamata iyaye su kula sosai da sosai acikin wannan yanayi na sanyi musamman tsaftar yaran da tufafinsu wajen kwanciyar su da sauran abubuwa makamanci hakan sannan kuma mukula sosai da kashe abin girki musamman mu da muke karkara Allah ya karemu ya sa mufita lafiya
Sulaiman Muhammad
A daina aiken yara da sanyin Safiya, A sanyawa yara kaya masu nauyi, Kowa da kowa yana shan tea mai zafi sama sama, A daina aje Gas inda iska take kadawa in za a yi girki, A daina shiga da gawayi cikin daki da niyar jin dimi kuma ayi barci ba tare da an kashe shi ba, Masu skil cell a kula dasu sosai, Allah yasa muga karshensa lafiya
Ra’ayi na musamman
Tashin Farashin Kayan-gona Yana Da Nasaba Da Chanjin Kuci.
Salam, Edita da masu karatu ina maku fatan alkairi, wato chijin kudi da gwamnati ke kokarin aiwatarwa tun yanzu talakan Nijeriya ya ga takansa abinci yana neman gagararmu wai kakar amfanin gona amma anawawar hatsi a kasuwa ina kuma tafiya ta yi nisa? Allah ka kawo mana agajinka ba don halinmu ba
Daga Umar-A-Umar Mazoji Matazu Katsina
07046493147