A wannan makon muna son jin ra’ayoyinku ne a kan ko yan kasuwa sun sassauta farashin kayan masarufi kamar yadda Malamai ke ta yi musu wa’azin a tausaya wa al’umma a cikin wannan wata mai alfarma? Muna addu’ar Allah ba mu ikon rubanya ayyukan alhairi a cikin wannan watan.
Sameenu Dahiru Abdullahee Dambatta
Amin ya Allah
Abubakar Ghali
Gaskiyane bana kam alhamdulillah an samu raguwar tsadar kayan masarufi, gaskiya mutane sun ji wa’azi musamman wa’azin mai girma baba major.
Ahmad Muhammad Rufai
Tabbas an sassauta, amma Banda ‘yan kasata Nijeriya.
Kabo Idris Saminu
‘Yan kasuwa dai suna da rawar da ya kamata su taka wajen ragewa al’umma wannan radadin da suke sha Allah dai ya basu zuciya taimakawa talaka ya gyara mana su.
Hadiza Bello Hamza
Lallai akwai bukatar ‘yan kasuwa su kara rage farashi kayan masarufi don talakawa su samu saukin gudanar da ibada, mun gode da wannan damar da kuke bamu, Allah ya saka da alhairi, amin summa amin
Zahara Murtala Sakkwato
Ina fatan wa’azozin da Malamai suke yi zai shiga jikin ‘yan kasuwa manya da kanana wajen rtage fasashin kayan masasrufi, musamman ganin yadda ake ninninka lada da zunubi a wannan watan mai alfarma, Allah y aba mu ikon gyarawa.
Barista Adamu Bello
Muna nan muna jirajn ranar da ‘yan kasuwa za su rage farashi a yankjinmu don har zuwa wannan lokacin duk abubuwan da farsshinsa ya tashi to har yanzu ya makale ya ki saukowa.
Murjanatu Mu’azu
Allah dai ya kawo mana karshen wadannan matsalolin, ksan duk ranar5 da ka tafi kasuwa sai ka ji farashin kaya ya canza, babu kuma wani dalili na yin haka. Ya dai9 kamata al’uma mu ji tsoron Allah, musamman a wannan watan mai alfarma.