• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ra’ayoyinku Da Fatanku Game Da Zaben Shugaban Kasa

by Aisha Seyoji
3 years ago
Zaben Shugaban Kasa

Barkanmu da sake saduwa daku a wannan fili namu, a wannan makon mun kawo muku ra’ayoyinku ne a kan abubuwan da kuke fata tattare da zaben shugaban kasa da zai gudana gobe Asabar 25 ga watan Fabrairu 2023.

 Mahdee Bashir

Allah ya zaba mana mafi alkhairi, amin. Amma ni tunda wannan jaririiyar damokaradiya taki girma, kullum kasar tana walagigi toh, Soja su karba su taba tunda mulkin ya fi kama da tasu, amma zababbu suna ta gasa mana aya a hannu.

Mohammed Inuwa

Muna fatan a yi zabe lafiya cikin salama. Kuma a yi gaskiya a bawa talaka daman zaben wanda yake so. Allah ya bamu shugabanni masu tausayin mu, ameeen

LABARAI MASU NASABA

Madallah Da Hutu Ga ‘Yan Sakandire Domin Azumi 

Ya Kamata A Biya Yaran Da Aka Gurfanar Saboda Zanga-Zanga Cikakkiyar Diyya – Ajiyan Yawuri

Sameenu Reina J Dambatta

Allah ya sa a yi wannan zabe lafiya, ubangiji ya zaba mana shugabanni nigari, ina kuma kira ga ‘yan uwana matasa da mu guji tayar da hayaniya a lokachin zabe, kada mu bari wasu su yi amfani damu wajen tada zaune tsaye

Sani Ladan

Alhmdulilahi, fatan mu a wannan zabe da zai gudana ya zamo zaben da ya fi kowanne alkhairi, saboda muna cikin bukatar irin wannan shugabanni a wannan lokacin Nijeriya da ‘ya’yanta sun shiga dimuwa kasancewar sun gwada shugabanni kala-kala amma har yanzu zancen guda daya ne, zan baku ruwa, wuta, lafiya da sauransu, kullum maganar kenan to muna addu’ar wannan karon ya zama shugaban da zai zo ya karar da wannan matsaloli kacokan, Allah ya sa mu dace da shugaba mai adalchi da aiki tukuru.

Baban Khairat

Fatan Alheri, a yi chanchantan a duba nagartaccen wanda ake wa kyakyawar zato ba tare da banbancin yare jinsi ko addini ba, sai kuma iyaye su ja wa ‘ya’yansu kunne kan shiga bangar siyasa da shaye-shaye, da fatan Allah ya sa ayi zabe lafiya kuma ya bamu shugaba nigari.

Muhd Basheer Sa’ad

Fatan mu Allah ubangiji ya sa zabin da zamu yi ya zamo mai amfani a gare mu. Ba mai amfanar kansa da iyalin sa ba

Rchp Ahmad Shehu Babaldu

Fatan mu da adduar mu shi ne ayi zabe lafiya, a gama lafiya. Allah ya kuma zaba mana shugabanni nagari.

Abubakar Mohammed Joda

Allah ya zaba mana mafi alkhairi kawai ita ce addu’armu. Domin kuma ‘yan takaran gaba dayansu maneji ne, wasu kuma basu da kafasitin cin zabe. Mun bai wa Allah zabi kawai.

Aisha Muazu

Babban fata dai ayi a gama lafiya, Allah kade fitina. Kowa na da wanda yake so da kuma dalilin son, fatan dai Allah ya zaba mana wanda ya fi zama alkhairi a garemu, ba son ran mu ba, Allah bamu ikon yin biyayya ga wanda zai ci zaben. Allah kawo mana saukin wannan yanayi da muke ciki

Fauziya Umar Dauda

Allah ya zaba Mana shugabanni nigari, ya sa a gama lafiya, amin.

Engr Abdullahi Musbahu Dambatta

Fatan mu dai Allah ubangiji ya sa ayi zabe lafiya a gama lafiya, Allah kuma ya zaba mana shugabanni nagari

Khadija Muhammad

Rahama Allah ya kasance tare dà mu a ranar zabe ya kuma shige mana gaba

Sani Bello Kano

To abin fada a nan shi ne, Allah ya zaba mana mafi alkhairi koda ba shi muke so ba tunda mun zabi wanda muke so da kyautata masa zato amma ya keramu ya sa muka yi nadama kamar bayi, yandu kam sai dai mu barwa Allah zabi, sai dai zamu je mu zabi wanda muke ganin shi ne dama dama da cancanta a cikinsu ‘yan takarar sanan mu bisu da addu’a sai mu barwa Allah sauran ko me ya yi dai-dai ne

Abubakar S G Diso

Aallah ya sa a yi lafiya a gama lafiya, Ubangiji Allah ya ba mu shugabanni nagari masu tsoron Allah a zuci, muma mabiyan Allah ya shirye mu.

Mariya Jika

Allah ya zaba mana shugabanni nagari

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Madallah Da Hutu Ga ‘Yan Sakandire Domin Azumi 
Ra'ayoyi

Madallah Da Hutu Ga ‘Yan Sakandire Domin Azumi 

March 18, 2025
Ya Kamata A Biya Yaran Da Aka Gurfanar Saboda Zanga-Zanga Cikakkiyar Diyya – Ajiyan Yawuri
Ra'ayoyi

Ya Kamata A Biya Yaran Da Aka Gurfanar Saboda Zanga-Zanga Cikakkiyar Diyya – Ajiyan Yawuri

November 10, 2024
Nijeriya
Ra'ayoyi

Ra’ayoyin ‘Yan Nijeriya A Kan Zagayowar Ranar Samun ‘Yancin Kai

October 5, 2024
Next Post
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Yi Gamsasshen Bayani Game Da “Nord Stream”

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Yi Gamsasshen Bayani Game Da “Nord Stream”

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

November 6, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

November 6, 2025
Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

November 6, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

November 6, 2025
Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

November 6, 2025
Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

November 6, 2025
Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.