Kamar yadda mu ka alkawarta cewa, za mu tattaro wasu daga cikin ra’ayoyinku a shafinmu na Facebook, LEADERSHIP A YAU, ga kadan daga cikinsu. Mun gode – EDITA
- Ummu-Aysha Ahmad
Shekaru 57 bayan samun ’yancin kan kasa daga Turawan Mulkin Mallaka shekaru ne na gwagwarmaya, shekaru ne na fadi-tashi, shekaru ne na kokarin tsayuwa da kafafu.
Shakka babu Nijeriya ta samu ci gaba gwargwado a tsayin wadannan shekaru ta fuskar siyasa, mulki, kasuwanci, aikin gona da sauran su. Amma a hakikanin gaskiya idan a ka kwatanta Nijeriya da wasu kasashe wadanda mu ka samu ‘yanci a lokaci daya za a ce ci gaban da aka samu ba muhimmi ba ne wanda har za a yi murna ko bukin tunawa.
Shekaru 57 da samun ‘yanci, amma har yanzu dimokuradiyar mu jaririya ce, shekaru 57 amma har yau tsarin mu na gudanar da zabe gurbatacce ne. Shin ba abin kunya ba ne a ce mun shekara 57, amma ba mu iya sarrafa albarkatun man fetur a cikin kasa ba? Matatun mu na mai gurbatacci ne a wadannan shekaru, amma hanyoyinmu na mota a lalace su ke. Hasalima sun zama tamkar tarkon mutuwa. Shekaru 57, amma mu na rayuwa ta cin hanci da rashawa, mu na rayuwa ta kisan ‘yan uwanmu, mu na rayuwa tamkar dabbobi, domin rayuwar mu babu bin doka ballantana oda.
Anya ba abin takaici da damuwa ba ne a ce shekaru 57 da fita daga kangin bauta amma har yau ba mu da tsarin kiwon lafiya ingantacce, asibitocin mu a lalace, babu kayan aiki, babu ma’aikata kwararru kuma babu magani ta yadda masu hannu da shuni sun mayar da zuwa Indiya da sauran kasashe wajen duba lafiya tamkar zuwa unguwa shi kuwa talaka da sauran marasa karfi su na nan a asibitin gida cuta na halaka su. Duka baya ga wannan tattalin arzikin mu a kullum a tabarbare ya ke.
A sha’anin Ilimi shekaru 57 amma iliminmu a tabarbare ya ke, jami’o’i da manyan makarantun mu ba su bayar da ingantaccen ilimi, ‘ya’yan manya a yau sun dogara da samun ilimi a jami’o’in kasashen waje ta yadda a yau ‘yan Nijeriya sun mayar da zuwa kasashen Malaysia, Indiya, Egypt, Ingila da Sudan da sauransu karatu saboda rashin ingantaccen tsarin ilimi a kasarmu.
Idan na juya a yankin da na fito, za mu ga cewar a iyasance samun ‘yancin kasa bakidaya a shekarar 1960 daga Turawan Mulkin Mallaka ya dogara ne kacokan kan hadin kai, kwazo, sadaukarwa da kuma jajircewar wasu daga cikin hazikan dattawan Arewa wadanda a kodayaushe tarihi ya na yabawa kwazonsu kan ilmantar da mutanen Arewa da dora su a kan turba mai kyau, irinsu Sir Ahmadu Bello da Sa Abubakar Tafawa Balewa wadanda su ka tafiyar da Arewa a matsayin tsintsiya madaurinki daya tare da kaita ga tudun mun tsira.
Sai dai a yau shekaru 57 bayan da Nijeriya ta zama ‘yantacciyar kasa bayan samun yancin kai har zuwa yau bayan shudewar wadannan tarin shekaru, kai tsaye a iya cewa akwai kalubale a gaban Nijeriya domin cigaba da bunkasar da ta samu a jiya ta nemi rabin rabinsa ta rasa a yau.
Kasancewar na fito daga yankin Arewa, a yau shekaru 51 bayan ban kwana da Sardaunan Sakkwato amma har zuwa yau a na tunawa da yadda Firimiyan ya gina Arewa tare da daga darajar al’ummar Arewa. Sai dai har zuwa yau shekaru 57 da samun ‘yanci ba a samu wani ko wasu daga yankin Arewa wadanda suka kama ko da kafar Sardauna ta fuskar karfin iko, kishin Arewa da shimfida ayyukan raya kasa a Arewa ba, baya ga mutunci, dattako da sanin ya kamata da Gamji Dan Kwarai ya rayu a kai.
Duk da cewar wadanda ke siyasa a yau a Arewa suna son a yi ta’alikin siyasarsu da siyasar Gamji Dan Kwarai, amma kasawar wasu daga cikin shugabannin Arewa wajen koyi da Ahmadu Bello ba zai rasa nasaba da karancin kishin Arewa, kwadayi da bukatar tara abin duniya ba, a daya bangaren tare da kabilanci, rikicin addini, sabanin zamantakewa da kuma na’ukan matsaloli irin na ‘yan mulkin mulukiyya, ko kuma ‘yan handama da babakere.
Idan mu auna cigaban da Najeriya ta samu tun bayan samun ‘yancin kai daga Turawan mulkin mallaka, za mu fahimci cewa, lallai Najeriya samu gagarumin cigaba ta fuskoki da dama, duk da wasu matsalolin da su ke yiwa kasar tarnaki.
Najeriya ta samu cikakken cigaba ta fuskar tabbatar da dimukradiyya a fadin kasar, musamman bayan dawowar mulki ga farar hula a shekarar 1999, wanda ya ke tun a wannan lokaci ne dimukradiyya ta samu gindin zama a Najeriya har kawo yanzu kuma mu na fatan hakan ya dore.
A fannin tattalin arziki kuwa, Najeriya ta cigaba matuka ainun. Kasancewar ta kasa mai cin gashin kan ta, ta yi kokarin ganin ta samar wa da kan ta hanyoyin habaka tattalin arziki da za ta dogara da shi. Misali a nan shi ne, hako man fetir a yankin kudancin kasar. Duk da dai, Najeriya ta na fama da matsalar cin hanci da rashawa da kuma masu rub-da-ciki da dukiyar kasa.
Fannin tsaro, lallai Najeriya ta cigaba ainun a wannan fannin, wanda yake, idan mu ka duba, Najeriya ta samar hukumomin tsaro daban-daban da za su kula da kare lafiyar ‘yan kasa da kuma dukiyoyinsu. Duk da ya ke a ‘yan shekarun baya bayan nan, ingancin tsaro a Najeriya ya ja da baya, amma a yanzu za mu iya cewa ya fara inganta.
Ta fannin noma da raya kasa ma, Najeriya ta yi zarra a wannan fanni a inda za mu lura cewa kowane fanni na Najeriya sun rika noma ka’in da na’in, musamman ma a wannan lokacin da mai girma Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya yi kira da ‘yan kasar nan, musamman matasa su koma gona. Kuma ga dukkan alamu ‘yan kasa su amsa kira. Domin kuwa sha’anin noma a kasar nan sai kara habaka ya ke yi. Idan mu ka duba, yankin Arewa sun yi shuhura wajen samar da kayan hatsi da sauran su. Yankin Kudanci kuwa, sun yi shuhura ne a fannin samar da abinci kamar doya da manja da ayaba da kwakwa da sauransu.
Alal hakika, Najeriya ta samu cigaba ta hanyoyi daban-daban daga lokacin samun ‘yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. Duk da ya ke kasar na fama da ‘yan matsaloli a tattare da ita. Amma kuma, ko kadan ba za mu ce zaman ta karkashin mulkin mallaka ne mafi a’ala ba. A’a ! Ya na da kyau mu fahimci cewa, shi kan shi samun ‘yancin kan daga Turawan mulkin mallaka wani gagarumin cigaba ne na musamman.
Da fatan Allah Ya kara ciyar da kasarmu Najeriya gaba.
- Comrade Nazifi Ubale Fagge Kano
Mu na godiya Edita Allah kara basira, amin. Ni a rayina an yi rurin ba mu ’yancin kai saboda har yanzu ban ga wani cigaba da a ka yi ba. Sai dai fatan mu shi ne, Allah Ya kawo ma na masu yi ma na adalci, amin.
- Murtala Abdullahi Muhammad Dansudu
Tabbas an samu cigaba fiye da lokacin da turawa ke mulkarmu, amma maganar gaskiya kamata ya yi a ce cigaban ya wuce haka. Duba da har yanzu wutar lantarki, ruwan sha, tsaro, lafiya, da ma tituna da ilimi har yanzu ba su inganta kamar yanda ya kamata ba. Da a ce shugabanninmu na baya sun sanya kishi da tsoron Allah a cikin zuciyarsu wallahi da yanzu mu kai matsayin sa’annin kashashe irin su Brazil, Indiya, Saudiyya da ma China amma ina!!!!!! To, amma yanzu mu na da yakini a kan cewa Allah ya fara dawo da hankalin shugabanninmu kan hanya a wannan gwamnatin. Mu na fatan Allah ya shiryar da mu da shugabanninmu, mu hadu domin ciyar da kasar gaba. Ameen.
Najeriya kasa mai albarka kuma wadda ta samu tagomashi a idon duniya. Mu na murna da kawowar Najeriya a cikin wannan turbar dimokaradiyya a yau.
- Daga Nura Mai Apple Gusau
Mun samu gagarumin cigaba a fannin ilimi da kuma bangaren kimiyya da fasaha da ma wasu ababe da mu ke gani a halin yanzu. Ko shakka babu wannan abin yabawa ne.
Saidai kuma kash!!! duk wadannan abubuwa a na iya moriyyarsu, amma in akwai zaman lafiya, Najeriya mun tsinci kanmu cikin wani mawoyacin hali na rashin tabbas a kan abubuwan da ke wakana a duk yinin Allah. Amma kuma mun yi imani da Allah Insha Allahu wata rana sai tarihi. Mu na fatan haka.
Mu na addu’ar Allah ya kara ba mu zaman lafiya , yalwar arziki da samun ingantattun shugabanni nagari, mu kuma talakawan, Allah ka ba mu ikwon yin biyayya ga shugabannin, ameen.