A makon da ya gabata ne, Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufa’i ya sha alwashin kakkabe duk wasu baragurbin ma’aikaci da ya cancanci a kore shi a gwamnatinsa da kuma rushe duk wani gini da ya cancanci rusau har zuwa ranar da zai yi bankwana da mulki.
Gwamna el-Rufa’i ya bayyana hakan ne a ranar Asabar lokacin kaddamar da littafi a kansa, wanda shahararren dan jarida, Mista Emmanuel Ado ya wallafa.
Gwamnan Jihar Kaduna ya kara da cewa zai ci gaba da yin rusau ne domin kawo gyara ta yadda magajinsa idan ya hau karagar mulki ba sai ya sha wahala ba.
Ya ce, “Duk wani abin da muka ga bai dace ba, za mu cire shi ta yadda gwamnatin da za ta zo bayanmu, ba za ta sake yi ba. Ku sanya ido ku gani har zuwa karshen wa’adin mulkinna, za mu ci gaba da korar baragurbin ma’aikata da rushe abubuwan da ba su dace ba,” in ji Gwamna el-Rufa’i.
Gwamnan ya bayyana hakan ne kwanaki kadan bayan da gwamnatinsa ta soke izinin mallaka na wasu kadarorin tsohon gwamnan jihar, Sanata Ahmed Makarfi, inda ta sanya musu alamar rushewa.
Lokacin da el-Rufa’i ya bayyana hakan, sai wasu suka dauka hakan ba zai yiwu ba, amma wadanda suka san hali suka ce lallai zai aika. Kwatsam san aka wayi gari da yin rusau a Gbagy Billa da ke Jihar Kaduna, inda al’umma suka shiga zakulo kayansu a cikin barazugan kango. Sanan kuma gwamnatin ta rusa wasu wuraren manya na almajiran Sheikh Zakzaky a Kaduna da Zaria a tsawan kwana uku daga Asabar zuwa Litinin.
Hakazalika, Gwamnan el-Rufa’i ya amince da tsige sarakunan Piriga da Arak, Mai Martaba Jonathan Paragua Zamuna da Mai Martaba Janar Aliyu Iliyah Yammah (Mai ritaya).
Kwamishiniyar al’amuran kananan hukumomin Jihar Kaduna, Hajiya Umma Ahmad ce ta bayyana tsige sarakunan guda biyu cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin ranar Litinin, inda ta ce sarakunan biyu sun daina gudanar da ofisoshinsu daga ranar Litinin 22 ga watan Mayun 2023.
Kwamishinan ta kara da cewa matakin tsige sun ya biyo bayan shawarwarin da ma’aikatar kula da kananan hukumomi ta yi bisa tanadin sashe na 11 na dokar da ta shafi sarautu mai lamba 21 ta shekarar 2021.
A cewarta, “Hakimin Garun Kurama, Babangida Sule shi ne zai kula da al’amuran masarautar Piriga har zuwa lokacin da za a nada sabon sarki, yayin da aka umarci sakataren majalisar da ya fara aikin nadin sabon hakimin.
“Sakataren majalisar masarautar Arak shi ne zai kula da al’amuran masarautar tare da kaddamar da tsarin nada sabon sarki,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa an tunbuke rawanin Janar Iliyah Yammah ne sakamakon saba ka’ida game da batun nadin hakimai hudu sabanin wanda aka amince da shi a masarautarsa da kuma rashin zama a masarautar Arak.
Haka kuma sanarwar ta ce an tsige Sarki Jonathan Zamuna ne biyo bayan rikicin kabilanci da ya barke tsakanin al’ummar Gure da Kitimi na Piriga a karamar hukumar Lere da kuma rashin zama a cikin masarautar.
A hannu guda kuwa, kungiyar ‘yan shi’a magoya bayan Sheikh Ibrahim Zakzaky ta yi Allah wadai da matakin da gwamnatin Jihar Kadunan ta dauka na rushe wa ‘ya’yan kungiyar gine-ginansu wadanda suka hada da makarantu da asibitoci da kuma gidaje da ke a fadin Jihar Kaduna.
Shugana kungiyar ‘yan shi’a reshen Jihar Kaduna, Aliyu Umar da ake yi wa lakabi da Tirmizi, ya shaida wa BBC cewa, ba su taba tsammanin irin wannan abu zai ci gaba ba, musamman a wurare na ilimi da asibiti, inda al’umma ke haduwa na neman lafiya.
Ya ce, ‘’ Mu a matsayinmu na ‘yan’uwa musulmi almajiran malam Zakzaky, muna da hakki mu mallaki duk abin da za mu mallaka a karkashin dokokin kasar nan.
“A yanzu babban matakin da za mu dauka shi ne, addu’ar Allah ya gaggauta daukar mana fansa, na biyu kuma za mu garzaya mu je kotu kuma an riga ma an kai kara ba a fara shari’a bane.”
Ganau sun ce da tsakar dare ne wasu ma’aikatan hukumar tsara birane ta Jihar Kaduna tare da rakiyar jami’an tsaro ne suka isa makaranta da wani asibiti mallakin wasu mambobin kungiyar shi’a magoya bayan Zakzaky suka rushe.
To sai dai kuma a nata martanin, gwamnatin Jihar Kadunan ta ce an dauki matakin rushe asibiti da makarantar ne saboda wasu dalilai.
Mai Magana da yawun hukumar tsara birane ta Jihar Kadunan, Nuhu Garba dan Ayamaka, ya shaida wa BBC cewa ko da mutum ya gina gini kuma yana da izini daga hukumarsu, daga baya aka ga ya saba wa doka bisa dalilai na tsaro, to hakkin hukumar ne ta dauki matakin da ya dace.
Ya ce, “Na farko an gina wuraren ne ba tare da izini ba, sannan kuma bisa dalilai na tsaro sai da muka aike musu da takarda a kan su a daina gudanar da wasu abubuwa da ake yi a wannan wurare.”
An dai jima ana takun saka tsakanin magoya bayan Sheikh Zakzaky da kuma gwamnatin Jihar Kaduna.
Wannan lamari yana faru ne yayin da ya rage kasa da ‘yan kwanaki gwamnan Jihar Kadunan, Malam Nasiru El-Rufai ya mika mulki ga wanda zai gaje shi.
Yanzu dai jama’a na ta addu’ar samun saukin wannan lamarin tare da neman sabuwar gwamnatin Jihar Kaduna ta duba lamarin da idon basira.