Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce rage tsadar rayuwa na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sanya a gaba.
A cikin jawabinsa na bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Nijeriya, Tinubu ya ce gwamnati za ta yi ƙoƙarin rage kuɗin da ake kashewa wajen samar da kayayyaki da kuma jigilar su zuwa sassa daban-daban na ƙasar.
Ya ce Nijeriya ta fuskanci sauye-sauyen tattalin arziƙi masu wahala cikin shekaru uku da suka gabata, kuma yanzu ƙasar na shiga wani sabon mataki da ya fi mayar da hankali kan bunƙasa tattalin arziƙi da wadata ‘yan ƙasa.
Tinubu ya kare matakan da gwamnatinsa ta ɗauka, ciki har da cire tallafin man fetur, yana mai cewa an ɗauke su ne domin magance matsalolin da suka daɗe suna addabar tattalin arziƙin ƙasar.
Ya ce gwamnati za ta mayar da hankali kan noma, samar da ayyukan yi, masana’antu, ababen more rayuwa da rage kuɗin sufuri domin sauƙaƙa rayuwar ’yan Nijeriya.
Ya ƙara da cewa rage kuɗin samar da kayayyaki da jigilar su zai taimaka wajen rage farashin kayayyaki da ayyuka.
Tinubu ya yarda cewa miliyoyin ’yan Nijeriya na fuskantar matsalar tsadar kayan abinci, ilimi, kiwon lafiya da sufuri.
Ya ce gwamnatinsa na ƙara shirye-shiryen tallafa wa marasa ƙarfi, bayar da rancen tallafin ilimi da kuma bashi ga ’yan ƙasa.
Shugaban ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziƙin, da nufin rage talauci da samar wa ’yan Nijeriya ci gaba.














