Jihohin Arewa guda bakwai sun ware tsagwaron kudi har Naira biliyan 28.3 domin ciyar da masu azumi a watan na Ramadan.
Jihohin guda bakwai sun hada da Katsina da Sakkwato, Kano, Jigawa, Kebbi, Neja da kuma Jihar Yobe.
- Sin Ta Nuna Fasahohin Zamani A Taron Baje Kolin Masana’antun Nukiliya Na Duniya
- Sojoji Sun Ceto Wasu Mutane Da Aka Yi Garkuwa Da Su Tare Da Kashe Wasu ‘Yan BindigaÂ
Bayanai sun nuna cewa akwai wasu karin jihohin Arewac da dama da su ma suka ware kudaden domin ciyarwa.
Wannan abu dai ya janyo kace-na-ce a tsakanin mutane, inda wasu malaman addinin ke kira da a yi bincike bisa lura da irin yawan kudaden da aka ware.
Jihar Katsina ce dai ta fi kowace jiha kashe kudin, inda ta ware Naira biliyan 10.
Sai kuma jihar Sakkwato da ta ware Naira biliyan 6.7, sannan Jihar Kano da ta fitar da Naira biliyan shida.
Ita kuwa jihar Jigawa ta fitar da Naira biliyan 2.83, sai jihar Kebbi da ta fitar da naira 1.5 biliyan.
Jihar Neja ta ware naira miliyan 976, yayin da Jihar Yobe, ta ware Naira miliyan 178 domin ciyarwar.