Sojojin rundunar Operation Hadin Kai, tare da haɗin gwuiwar ‘Yan Bijilanti (CJTF), sun kashe adadi mai yawa na ‘yan ta’addar Boko Haram/ISWAP a wasu hare-haren da suka kai a jihar Borno.
A cikin wata sanarwa da Sojojin Nijeriya suka fitar ranar Alhamis, an bayyana cewa Sojojin sun mayar da martani ne kan wani leken asiri game da yunƙurin ‘yan ta’addan na kwace kayan abinci daga wata mota ta farar hula a kusa da Rann, shalƙwatar ƙaramar hukumar Kala-Balge.
- Mutum 3 Sun Rasu, Wasu Sun Jikkata Yayin Da Bama-bamai Suka Tashi A Hanyar Borno
- Gasar Wasanni Ta Kasa: FCT Ta Lallasa Borno Da Ci 4-1 A Wasan Farko
A yayin wani hari, Sojojin sun kashe ‘yan ta’adda shida kuma sun kwato bindigogi irin na AK-47 da harsasai. Wani jami’in Soja da ba ya son a bayyana sunansa ya ce farke layar tasu ya hana ‘yan ta’addan kwace wasu kayayyakin abinci da aka tattara don al’ummar yankin.
A wani harin na daban, Sojojin da ke aiki a Molai tare da CJTF sun yi kwanton ɓauna a wani wurin da ‘yan ta’adda ke amfani da shi wajen ketare kusa da Komala, kan hanyar Maiduguri-Damboa.
Harin ya janyo kashe wasu ‘yan ta’adda, kuma an kwato wasu babura, da kayan haɗa bama-bamai, da sauran kayayyaki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp