Fitacciyar mai ba da shawara kan zamantakewar aure da kuma rayuwa kuma marubuciya, Khadija Ibrahim, wadda ta jima tana gyara zamantakewar al’umma da alkalaminta, ta shirya kaddamar da sabon littafinta mai suna ‘100+ Questions Before Nikkah’ a ranar Asabar.
Littafin zai amsa tambayoyi dari da dori ga mata da maza da suke bukatar sani kafin shiga daga ciki.
- Nijeriya Da Saudiyya Sun Yi Kunnen Doki A Wasan Sada Zumunta
- Ba Zan Yi Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ba – Gwamna Lawal
Za a kaddamar da littafin a ranar Asabar, 14 ga watan Oktoba 2023, a dakin taro na Babban Masallacin Kasa da ke Birnin Tarayya, Abuja, da misalin karfe 10 na safe.
Marubuciyar ta rubuta littafin ne game da aure, wanda tambayoyin cikinsa za su fitar da samari da ‘yan mata masu shirin yin aure daga duhu kan sha’anin aure da abin da ya kunsa.
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ne babban bako na musamman, yayin da Sheikh Abu Mazeedatul Khaiyr bin Rauf, zai jagoranci kaddamar da littafin.
Bako mai jawabi, Ustaz Dakta Abulfattah Adeyeme, yayin da tsohuwar ministan jin-kai, Hajiya Sadiya Umar Faruk za ta kaddamar da littafin.
Mai girma Barden Kudu Zazzau, Malam Bashir Abubakar (MFR) zai kasance uban taron.