Duk shekara, ranar 26 ga watan Agusta ana gudanar da bikin Ranar Hausa ta Duniya, domin girmama da kuma ɗaukaka Harshen Hausa, wanda yake ɗaya daga cikin manyan harsunan Afirka da ake amfani da shi a sassa daban-daban na duniya.
Wannan rana an fara ta ne a shekarar 2015, wanda fitaccen ɗan jarida Abdulbaqi Aliyu Jari, ya shirya domin wayar da kan al’umma game da darajar harshen Hausa, musamman a kafafen sada zumunta.
- Sojoji Sun Kama Mutane 69 Masu Fasa Bututun Mai A Yankin Neja-Delta
- Za A Watsa Shirin “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” a Manyan Kafofin Watsa Labarai Na Kasashen SCO
Babban manufar wannan rana ita ce bunƙasa haɗin kai da fahimtar juna tsakanin masu amfani da harshen Hausa.
Ana kuma jan hankalin jama’a kan yi amfani da harshen Hausa a rubuce-rubuce, a tattaunawa da mu’amala, musamman a shafukan sada zumunta.
Wannan ya sa ake ganin Ranar Hausa ta Duniya a matsayin wata hanya ta kare harshen da kuma ƙarfafa amfani da shi a fannoni na zamani kamar kimiyya, fasaha da kasuwanci.
Bikin ranar ba iya Nijeriya kawai ya tsaya ba. Ana gudanar da bikin a ƙasashe da dama irin su Ghana, Amurka, Turkiyya da kuma Dubai, inda al’ummar Hausawa ke yin rayuwa.
A waɗannan wurare, ana shirya wasanni irin gargajiya kamar wasan Dambe, nuna abinci da kayayyakin al’adu, da kuma gudanar da taruka, tattaunawa kan harshen Hausa da tarihinsa.
A Nijeriya, cibiyoyi da ƙungiyoyi masu zaman kansu sukan shirya taruka da laccoci.
A jami’o’i irin su Jami’ar Bayero ta Kano da sauransu, masana da ɗalibai su kan tattauna kan ci gaban Hausa a fannin kimiyya da fasaha, da kuma ƙirƙiro sababbin kalmomi da ke dacewa da zamani.
Haka kuma, jama’a na amfani da wannan rana a kafafen sada zumunta domin wallafa karin magana, hotuna da kayan al’adu, ko kuma rubuce-rubuce da ke nuna tumbatsar harshen Hausa.
Al’ummar Hausawa da ke ƙasashen waje su kan yi shagulgula da suka haɗa da rawa, waka, da sauran nau’ikan nishaɗi na gargajiya, abin da ke ƙara ƙarfafa zumunci a tsakaninsu.
Ranar Hausa ta Duniya ba ta zama lokaci na tunawa da harshen Hausa kaɗai ba, har ma da al’adu, kasuwanci da tarihin yadda harshen ya haɗa mutane da dama.
Ita ce rana da ke nuna alfahari da asali, tare da nuna irin rawar da Hausa ta taka wajen bunƙasa ilimi da ci gaban zamani.
Wannan yana ba da damar kallon harshen Hausa a matsayin abub alfahari da ya kamata a kula da shi tare da bunƙasa a nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp