Idris Aliyu Daudawa" />

Ranar Kula Da Hakori: Masana Sun Yi Kira A Kawo Gyara

Kungiyar masana cututtukan da suke da nasaba da hakori ta kasa rashen asibitin koyarwa na jami’ar Nsukka, raeshen Ituku-Ozala, ya yi kira da gwamnatocin tarayya da kuma jihohi da cewar su taimaka wajen samar da kudade, wadanda kuma za ayi amfani dasu saboda a kara inganta cibiyoyin horarwa wadanda suma za su taimaka ne wajen wayar da kan al’ummar Nijeriya, su san wasu ayyuka na Orthodontists.
Dokta Nkiru Folaranmi wadda ita ce Shugabar kungiyar ta kasa kuma har bila yau shugaban sashen kulawa da lafiyar hakoaran kananan yara na asibitin koyarwar, shine wanda ya yi wannan kiran cikin bayanin daya gabatar, ranar da aka bikin ranar lafiyar hakora ta duniya. Shi dai wannan bikin an yi shine a jamiar Nijeriya wadda take da zama a Enugu.
Folaranmi dai an ji tana kira da kamfanonin inshorar lafiya na kasa da cewar su dauki nauyin kulawa da a kalla yara wadanda suka kai shekara goma sha takwas (18).
Ta bayyana cewar ita ranar ana yin bikin tane saboda taimaka wajen yadda al’umma za su, san wasu al’amura dangane da cututtukan da suka shafi hakora.
Ta cigaba da bayanin cewar su Orthodontists sune wadanda suka cancanta, su duba su kuma bayar da magungunan da suka dace na, matsalolin malocclusion ( wato irin halin da hakoran sama dana kasa suke, musamman lokacin da suka hade) a tsakanin yara da kuma manyain .
Folaranmi ta kara bayanin ita manufar wannan bikin bata wuce saboda a wayar da kan al’umma, wajen gane ayyukan su wadannan kwararrun, da kuma amfanin yin gyara, idan da akwai wata matsala wadda ta shafi hakora da kuma kulawa da wata matsalar hakori kyauta, sai kuma duba idan da akwai wata matsala, sai kuma bayar da shawarwari. idan da akwai.
Kamar dai yadda ta kara bayar da haske cutar malocclusion na iya sanadiyar mutum ya kasance cikin wani hali na,bai da wani tabbas, ko kuma ya rika yin dari dari da shiga jama’a saboda yadda yadda halittar ta shi zata canza a sanadiyar ita cutar. Don haka akwai bukatar ayi kokarin kawo gyara idan da akwai matsala.
“TIta kungiyar kasa da kasa ta ware ranar 15 ga watan Mayu na ko wacce shekara, saboda ayi biki na kulawa da lafiyar hakora ko kuma the Orthodontic World Health Day, taken bikin wannan shekara shine “Orthodontics – samar da dama ta yin murmushi ga kowa da kowa, ba kuma tare da la’akari da shekaru ba ”.
“Kungiyar masana cutar data shafi hakora ko kuma Orthodontists tare da hadin kai dakungiyar ta duniya, sun ware ranar 15 ga watan Mayiu na ko wacce shekara, saboda wayar ma al;’umma kai, dangane da matsalar da za a iya shiga akan rashin daukar mataki wajen maganin cutar ‘malocclusion’.

Exit mobile version