Da alama har yanzu tsugune ba ta kare ba duk da karin albashin da Gwamnatin Tarayya ta sanar da kashi 25 zuwa kashi 35 ga ma’aikatanta, ana jajebirin bikin ranar ma’aikata ta shekarar 2024, yayin da Shuga-ban Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC), Kwamared Joe Ajaero ya bayyana cewa karin da gwamati ta ce ta yi ba zai yi wani tasiri bai dan aka duba halin da kasar take ciki a yanzu.
Kwamared Ajero wanda ya yi bayanin haka a ranar Laraba a wani shirin gidan talabijin na Chan-nels, ya bayyana cewa, su babban abin da suke so shi ne gwamnati ta yi musu karin kudin da zai ishi ma’aikaci ya rayu a kasar nan ba kawai karin da zai ci gaba da tsunduma shi a cin bashi ba kullum.
- Ranar Ma’aikata: Bayan Cike Giɓin Albashin Da Muka Gada, Za Mu Ci Gaba Da Inganta Walwalar Ma’aikata – Gwamnan Zamfara
- Ranar Ma’aikata: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Laraba A Matsayin Hutu
“Mu abin da muke bukata shi ne albashin da za a iya biyan ma’aikaci yar ayu a Nijeriya. Kuma akalla shi ne a biya shi Naira 615,000. Kuma wannan ma a lissafin da muka yi ne kafin abubuwa su kara tsada irin na kwanan nan. Daga ciki a wata akalla ma’aikaci zai iya kashe Naira 110,000 a kan sufuri kawai, kudin wuta Naira 20,000 (wannan ma kafin a sanar da karin kudin wutar da aka yi kwanan baya ne). Sannan ma’aikacin da yake da akalla iyali mutum shida zai iya kashe Naira 50,000 a kiwon lafiya, shi ma idan babu tiyata ko wata lalaurar rashin lafiya da za ta ci kudi sosai. Haka nan kudin haya, ma’aikaci na bukatar biyan akalla Naira 40,000 duk wata, haka nan yana bukatar akalla Naira 20,000 na sayen fetur da kananzir a wata, ga batun abinci da kudin makaran-ta da kayan marmari da sauransu. Duka idan aka hada lissafi ya kamata a biya ma’aikaci Naira 615,000 don ya iya rayuwa a Nijeriya. Wanda bai amince da hakan ba kuma zai iya zuwa kasuwa da kansa ya yi safiyon kudaden abubuwan da muka ambata.” Ya bayyana.
Shugaban ‘yan kwadagon ya kuma yi nuni da cewa karin albashi don ya dace da yanayin da ake ciki a kasa abu ne da ake yi a duk fadin duniya, don haka bai kamata gwamnatin Nijeriya ta zama daban a cikin dangi ba, inda ya yi kira ga ma’aikata su kara jajircewa wajen cimma nasarar abubuwan da suka tasa a gaba na ganin an inganta walwalarsu.
A ranar Talata da dare ne dai, Gwamnatin Tarayya ta sanar da karin albashi da kashi 25 zuwa 35 ga ma’aikatanta wanda ta ce zai fara aiki tun daga ranar 1 ga Janairun 2024. Abin da ya rage dai yanzu shi ne lokacin da gwamnatin za ta biya bashin albashin da kuma dorewa da biyan karin, kasancewar har yanzu akwai masu bin bashin alawus na Naira 35,000 da ta ce za ta ba kowane ma’aikaci don rage radad-in cire tallafin maid aga watan Satumbar 2023.