Yau ranar 1 ga watan Oktoba, rana ce ta cika shekaru 73 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, wadda kuma ta yi daidai da ranar cika shekaru 62 da samun ‘yancin kan Nijeriya, ranar da ta alakanta kasashen biyu da ma al’ummunsu ta wata hanya ta musamman, duk da nisan da ke tsakaninsu.
Tun bayan da kasashen biyu suka kulla huldar diplomasiyya a shekarar 1971, sun aiwatar da hadin gwiwa ta fannonin siyasa, da tattalin arziki, da al’adu, da kimiyya da dai sauransu, tare da cimma gaggaruman nasarori.
A ranar 1 ga watan Yulin bana, jirgin ruwa na farko ya isa tashar ruwa ta Lekki da ke Lagos wadda ake ginawa, daga bisani, shugaban tarayyar Nijeriya Muhammadu Buhari ya fitar da sanarwa, inda ya bayyana murna, da farin ciki, game da yadda jirgin ya isa wannan tashar ruwa ta zamani irinta ta farko a Nijeriya, wadda kamfanin kasar Sin ke daukar nauyin ginawa.
Ya ce, tashar za ta samar da dimbin guraben aikin yi bayan da aka fara aiki da ita, baya ga kuma yadda za ta kyautata rayuwar al’ummar Nijeriya, tare da sa kaimin harkokin cinikayya a tsakanin Nijeriya da kasashen ketare, wanda hakan zai taimaka ga kyautata yanayin kasuwanci na kasar tare da janyo karin jarin waje.
A watan Agustan da ya gabata kuma, kasashen biyu sun cimma yarjejeniyar kafa tsarin hadin gwiwa a tsakanin asibitin jami’ar Peking ta kasar Sin, da ma asibitin jami’ar Abuja na Nijeriya, a wani kokari na inganta hadin gwiwar kasashen biyu ta fannin kiwon lafiya.
Sai kuma a watan Agusta, lokacin da aka kaddamar da mataki na biyu na aikin kafa fitilu masu amfani da hasken rana na ba da hannu ga motoci a birnin Abuja…
Dukkan wadannan wani bangare ne kawai na nasarorin da aka cimma a hadin gwiwar kasashen Sin da Nijeriya. Da tashar ruwa ta Lekki, da layin dogon Abuja-kaduna, da filin jiragen sama na Lagos, da tashar samar da wutar lantarki ta Zungeru, da kuma musayar kudade tsakanin kasashen biyu, da hadin gwiwar harba taurarin dan Adam da binciken teku, lallai hadin gwiwar kasashen biyu ya shafi fannonin tattalin arziki, da al’adu, da ba da ilmi, da kiwon lafiya, da hada-hadar kudi, da kimiyya da sauransu, wanda ya haifar da hakikanin alfanu ga al’ummar kasashen biyu.
Ranar 1 ga watan Oktoba, ta shaida yadda kasashen biyu suka yi gwagwarmayyar fita daga mawuyacin halin da suka samu kansu a ciki a baya, tare da bude sabon babinsu.
Muna da imanin cewa, bisa shawarar “ziri daya da hanya daya”, da ma tsarin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, kasashen biyu za su karfafa dankon zumunci tsakaninsu, kuma hadin gwiwar kasashen biyu zai haifar da karin nasarori, da ma alfanu ga al’ummunsu. (Mai Zane: Mustapha Bulama)