Gwamnatin Jihar Kano ta shirya taron kara wa juna sani a wani bangare na bukukuwan cikar Nijeriya shekara 64 da samun ‘yancin kai.
Taron wanda ya mayar da hankali kan irin ci gaban da aka samu da kalubalen da ke addabar kasar nan, ya gudana ne a dakin taro na fadar Gwamnatin Kano.
- Kirkirar Kimiyya Da Fasaha Ta Kasar Sin Na Sa Kaimi Ga Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya
- Muhimman Abubuwa 10 Da Jawabin Tinubu Na Ranar ‘Yancin Kai Ya Kunsa
Da yake jawabi a wurin taron, Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya tabo batutuwa masu motsa zuciya, inda ya bayyana cewa bisa sake fasalin shugabanci da tabbatar da rikon amana, Jihar Kano ta zama madubi ga jihohi da kuma fagen ci gaban siyasar kasar nan.
Gwamna Abba bayan jinjina wa kokarin kwamitin da ya tsara wannan taro, wanda ya ce ya yi kyakkyanwan hange da tunanin zakulo masu gabatar da jawabai wadanda suka kasance mutane masu kima da daraja, ya yi karin haske kan kyakkyawan salon shugabancin gwamnatinsa.
Ya ce gwamnatin ta mayar da hankali sosai kan wasu muhimman ayyuka da suke da alaka da kyautata rayuwar al’ummar Jihar Kano kai-tsaye.
“Zan yi amfani da wannan dama domin bayyana wasu daga cikin manyan nasarorin da gwamnatin Kano ta samu a bangarori daban-daban, wannan kuma wani kokari ne na magance kalubalen da ya jima yana addabar rayuwar mazauna Kano.
“A bangaren ilimi, mun samu gagarumar nasarar sake farfado da sashin, hakan ya hada da ginawa tare da gyaran makarantu, daukar kwararrun malamai, samar da kayan koyo da koyarwa, haka kuma mun bujiro da tsarin ilmantarwa ta hanyar fasahar zamani da koyar da sana’o’i ga matasa.
“Sashin lafiya na cikin bangarorin da wannan gwamnati ke bai wa kulawa ta musamman, ta yadda aka daga darajar cibiyoyin kiwon lafiya, da kyautata tsarin kula da lafiyar mata masu ciki da kananan yara, kana an kuma yi duk mai yiwuwa wajen ganin ba a bar jama’ar karkara a baya ba. Sai kuma yadda muka tunkari kalubalen cututtuka kamar maleriya, karancin abinci mai gina jiki da sauran cututtukaka masu yaduwa.”
Har ila yau, Gwamna Abba ya nunar da cewa, sauran bangarorin da ke samun kyakkyawar kulawa a gwamnatinsa sun hada da sashin noma, tsaro, tallafa wa matasa da jari iri daban-daban, inganta tsarin aikin gwamnati da bayar da fifiko wajen biyan basussukan kudaden fansho da aka danne wa masu na tsawon lokaci.
Gwamnan ya kuma bayyana irin gagarumar nasarar da suka samu ta fuskar manyan ayyuka kamar kyautata muhalli, inganta harkar wasanni wadanda suka samar wa Jihar Kano gagarumin ci gaba.
Ya jaddada bukatar hadin kai a tsakanin al’ummar Jihar Kano domin kara samun nasarar da ake fata, yana mai cewar, “wannan kuma bai zai samu ba sai ta hanyar jajircewa, sadaukar da kai domin kare kimar al’ummarmu.” In ji shi.