Rashin Adalci Ne Silar Rashin Zaman Lafiya A Nijeriya –Abdulsalami Abubakar

Tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Abdulsalami Abubakar, ya bayyana cewa babu yadda za a iya samun zaman lafiya ba tare da adalci ba a Nijeriya.

Abubakar ya bayyana hakan ne jiya Litinin a yayin da ya ke bude taron sanin makamar aikin da aka shirya wa alkalan kotun majistare da kotunan yankuna na jihar Neja.

‘Idan babu adalci a kasa, to fa babu yadda za a iya samun zaman lafiya. Kuma babban abin da mu ke bukata yanzu a kasar nan shi ne zaman lafiya. Saboda idan babu zaman lafiya, ko taron nan ba za mu iya halarta ba. Don haka ya na da matukar zama tilas cewa wannan sanin makamar aiki da ake yi muku, to ku sani cewa sanin makamar shimfida wa mutane adalci ne ake koyar da ku. Ina matukar maraba da kuma goyon bayan wannan horaswa da ake yi muku ku kananan alkalan kotunan jihar nan. Allah ya sa irin wannan bada horo ya dore nan gaba.’ Inji Abdulsalami.

Janar din ya ce wajibin kowane dan Najeriya ne ya tabbatar da cewa an samu tsaro a fadin kasar nan. Daga nan sai ya jinjina wa gwamnatin jihar Neja saboda hangen nesan ta na shirya wannan horaswa ga alkalan kananan kotunan jihar Neja.

A nasa bayanin, Cif Jojin Jihar Neja ya ce wannan ne karo na farko da aka taba shirya wa alkali irin wannan horon sanin makamar aiki.

Exit mobile version