Daga El-Mansur Abubakar, Gombe
Rashin fitowar Mata a dama da su a siyasa musamman a jihar Gombe abun takaici ne domin har kullum ana barin mu a baya kuma mune rabin al’umma inji Hajiya Zariyatu Abubakar Hashidu.
Hajiya Zariyatu Abubakar Hashidu, ita ce shugabar kungiyar nan da ba ta gwamnati ba ta Wildan Care Foundation, ita ta bayyana hakan a Gombe a lokacin da kungiyar ta ta kai ziyara tsangayar yan jarida dake fadar jihar Correspondent’s Chapel dan bayyana korafinsu akai.
Ta ce an bar Mata a baya Mazaje basa barin Matansu su fito a dama da su a siyasance bayan kuma sune suke da rinjaye a cikin al’umma sannan kuma ba’a kulawa da su wajen basu mukaman da suka kamata idan aka kafa gwamnati wanda hakan tasa suke so Mata su taso su tsaya da kafarsu dan ganin sun kwatowa kansu yanci.
“Ko tuki Mace take yi da ta wuce sai kaji an ce Mace ce to kaga ana dakushe ta kenan maimakon a karfafa mata guiwa”inji Zariyatu.
Shugabar ta Wildan Care Foundation, taci gaba da cewa a jihar Gombe da akwai Mata Yan Majalisa har guda biyu maimako duk lokacin da akayi zabe a samu kari sai aka wayi gari biyun ma babu yanzu cikin yan Majalisa sama da ashirin babu Mace ko daya.
“Ina kiran Mazaje da babbar Murya na ganin suna barin Matansu suna fitowa a dama da su a siyasa tunda suna barinsu suyi aikin gwamnati me yasa ba zasu basu dama su fito siyasa ba, kar su tauyewa yan uwan mu Mata yanci a duba fa’idar hakan a barsu su fito a fafata dasu ba gasa mu ke yi da Maza ba”Tace hakan.
Daga nan sai Hajiya Zariyatu tace idan ba’a samu karin yawaitar Mata a siyasa ba babu yadda za’ayi a samu kason da ake so na Mata masu rige da mukaman gwamnati ba’a jihar Gombe kadai ba a ko’ina a Najeriya.
Sannan sai ta yi amfani da wannan damar tayi kira ga hukumo da gwamnatoci har ma da Mazaje wajen bai wa Mata yancinsu na yin takara da kuma bari a zabesu ba tare da nuna musu wata tsana ko kushe ba.