Daga Mustapha Ibrahim, Kano
An bayyana cewa rashin tsoran Allah da rashin gaskiya ne ke kawo cikas a harkokin kasuwanci da ma sauran harkokin yau da kulum. Wannan jawabin ya fito ne daga bakin daya daga cikin masu fada a ji, Alhaji Danlami Alassan Sabon Titi Kano, a lokacin wani taron na dulla zumunci da da inganta harkar zamantakewar aure a wannan lokaci.
Ya ce, ba wani abu ba ne zai kawo martabar kasuwanci da sauran mu’amalarmu ba sai ta hanyar sanya tsoran Allah da kuma gaskiya a harkar kasuwanci da sauran mu’amala na zamantakewa kamar aure da sauran al’umma na rayuwa a wannan zamani, inda ya shawarci ’yan kasuwa da su sanya sanin ya kamata a saye da siyarwarsu a guji ha’inci da tsauwalawa jama’a tsada a kasuwanni da sauran wajazan saye da sayarwa.
Ya ce, duk wani abu da ka saya cikin sauki ka sayar cikin sauki, to Allah zai sa albarka a cikin lamari, inda ya ce tsada bada kawo tarin dukiya, inda kuma ya bukaci gwamnati ta duk iya kokari na ganin an samu Dala cikin sauki, wanda ita ma hanya ce ta rage zafin radadin da jama’a ta ke ciki.
Haka kuma a karshe ya yabawa wakilan shugaban kasa Muhammadu Buhari wato shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da gwamna Zamfara Abdulaziz Yari da kuma Sanata Sani Ahmad Yariman Bakura wadda su ka halaci wannan mahimmin taro da a ka gabatar da shi a Kano wadda ya tabbatar da cewa tsakanin shugaban kasa da Kano akwai girmamawa da kamar yadda ta ke tsakanin Zamfarawa da Kanawa akwai kyaukyauwar alaka ta shekara da shekaru.