Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya bayyana damuwarss kan ƙaruwar rashin haɗin kai tsakanin ‘yan Nijeriya, inda ya yi gargaɗin cewa rashin zaman tare na barazana ga makomar ƙasar nan.
Da yake magana a lokacin taron buɗa-baki da Hakiman Zazzau, Sarkin ya jaddada buƙatar yin sulhu da haɗin kai don magance rabuwar kai da ke ƙaruwa a tsakanin al’umma.
- Fashewar Gas Ta Hallaka Yaro, Ta Jikkata Mutum 21 A Kano
- EFCC Ta Kama ‘Yan China 4, Da Wasu Mutum 27 Kan Zargin Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Jos
“Dole ne mu haɗa kai mu ƙarfafa zaman lafiya. Idan mun yi wa wani laifi, ya kamata mu nemi gafara. Rike ƙiyayya ba zai haifar mana da alheri ba illa ƙara rura wutar rarrabuwar kawuna,” in ji shi.
Ya jaddada cewa haɗin kai shi ne ginshiƙin ci gaba da zaman lafiyar al’umma, inda ya gargaɗi cewa idan aka ci gaba da rarrabuwa, ‘yan baya ne za su fi shan wahala.
“Ba tare da haɗin kai ba, ba za mu iya samar da kyakkyawar makoma ga mutanenmu ba. Idan muka ci gaba da tafiya a haka, za mu bar wa ‘yan baya gado mai cike da rikici,” in ji shi.
Sarkin ya kuma nuna damuwa kan yadda alaƙar abokai da ‘yan uwa ke rushewa, inda ya bayyana cewar mutane da dama sun daina kula da juna ko nuna damuwa ga halin da kowa ke ciki.
“Wannan ba matsala ce kawai a Zariya ko Jihar Kaduna ba—duk Arewacin Nijeriya matsalar ta shafa. Ƙalubalen da muke fuskanta a yau sun yaɗu, kuma sai mun haɗa kai domin samun mafita,” in ji shi.
Taron buɗa-bakin ya haɗa dukkanin Hakiman Zazzau da Sakataren Gwamnatin Jihar, wanda ya wakilci Gwamnan Kaduna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp