A ranar 29 ga Nuwambar 2023, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kudurin kasafin kudin shekarar 2024; ga majalisun dokoki na kasa, inda ya bayyana cewa za a kashe kimanin Naira tiriliyan 27.5, wanda daga baya majalisar ta mayar da kasafin zuwa Naira tiriliyan 28.7.
Haka nan, shugaban ya yi ikirarin cewa kasafin mai taken ‘Budget of Renewed Hope’, zai kawo bunkasar tattalin arziki, samar da ayyukan yi, daidaita tattalin arzikin kasa, samun ingantaccen yanayin saka hannun jari, habaka jarin Bil’adama, rage talauci da kuma samun zaman lafiya. Sai dai a gefe guda kuma, idan aka yi la’akari da kasafin kudin za a ga cewa ya fallasa kwadayin wadanda suka rubuta shi da kuma wadanda suka rattaba hannu a kansa tare da rashin tausayi da kuma cin amanar al’ummar Nijeriya.
- Ina Rubutu A Kan Rayuwar Yau Da Kullum Domin Mutane Su Wa’azantu – Fatima Sunusi
- Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Yadda Dalibai Za Su Samu Bashi
Mu duba kasafin kudin dangane da abin da Fadar Shugaban Kasa da Majalisar Dokoki za su yi awon gaba da su da kuma sauran abin da zai yi rara, wanda shi ne sauran ‘yan Nijeriya miliyan 240 za su raba tare da kuma tabbatar da tsaron wannan kasa.
Wani hanzari ba gudu ba, kashi nawa ne aka samu a kasafin kudin bara da ya shafi manyan ayyuka ?
Shin Wace Wainar Aka Toya A Kasafin Kudin Da Ya Shafi Majalisun Dokoki?
Daya daga cikin manyan matsalolin da ke tattare da kasafin kudin 2024 shi ne, makudan kudaden da aka ware wa majalisar dokoki ta kasa, kimanin Naira biliyan 344.85; wannan ya nuna karin kashi 74.23% daga cikin Naira biliyan 197.9 da Shugaban Kasa ya gabatar, kuma shi ne mafi girma a tarihin majalisar.
Manazarta dai sun kasa bayar da hujjar wannan gagarumin karin, wanda yake zuwa a lokacin da wasu bangarori masu muhimmanci ke bukatar kudade. Misali, kasafin kudin da aka ware don bai wa miliyoyin daliban Nijeriya lamuni; bai taka kara ya karya ba tare kuma da hasashen alherin da ke tattare da wadannan dalibai, wadanda su ne shugabannin kasar a nan gaba; idan aka kwatanta da kasafin kudin majalisun da kuma abin da ka iya fitowa daga kudirorin da za su gabatar, za a ga cewa lallai kam ba a kwatanta adalci ba.
Wani misali kuma shi ne, adadin da aka ware wa ma’aikatar agaji da rage radadin talauci, an rage shi zuwa Naira biliyan 131 daga Naira biliyan 201. Haka nan ma, ma’aikatar harkokin ‘yan sanda ta samu Naira biliyan 969, idan aka kwatanta da kalubalen da ‘yan Nijeriya ke fuskanta da kuma kayan aikin da ‘yan sandan ke bukata, tabbas wadannan kudade digo ne a cikin teku.
Ba abin mamaki ba ne idan wadannan ma’aikatu biyu suka kasa gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Haka nan, idan aka yi la’akari da kasafin kudin kiwon lafiya da ilimi da noma wadanda ke da matukar muhimmanci ga walwala da ci gaban ‘yan kasa, kasonsu ya yi kasa da ka’idojin kasa da kasa da kuma alkawuran da Nijeriya ta rattabawa hannu, kamar na Abuja a 2001,sanarwar da ke bukatar kashi 15 cikin 100 na kasafin kudin da za a ware wa kiwon lafiya da kuma sanarwar Maputo na shekarar 2003 da ke bukatar kashi 10 na kasafin kudin da za a ware ga aikin noma.Wannan ya nuna karkatacciyar manufa da rashin adalci a rabe-raben albarkatun kasa . Don haka, ya kamata majalisa ta kiyaye da biyan bukatun jama’a; ba kawai kokarin azurta kanta ba.
Wane Shagali Za A Yi A Fadar Shugaban Kasa?
Yin nazari wajibi ne a kan kasafin kudin da aka ware wa Fadar Shugaban Kasa da kuma lura da shin wannan rabon da aka yi an yi la’akari da halin da al’umma ke ci na kalubalen zamantakewa da tattalin arziki da suke ciki a halin yanzu kuwa? Ko kuwa an tabbatar da cewa, shugaban kasa ya dunkule cikin jin dadi ne, a yayin da talakawa ke fuskantar mawuyacin hali na rayuwar yau da kullum, ciki har da faduwar darajar Naira, karin farashin man fetur da rashin daidaituwar farashin man da hauhawar farashin kayayyaki da tsadar komai ciki har da gishirin miya.
A yayin da tawada ke bushewa a kan kasafin kudin shekarar 2024 da aka rattabawa hannu na Naira tiriliyan 28, ‘yan Nijeriya sun fara ganin cewa kasar na cikin wani hali na kuncin rayuwa, inda wasu sassa ke tabarbarewa ta fuskar rashin ababen more rayuwa, sabanin yadda ake samun wadatar arziki a hannun wadanda karagar mulki ke hannunsu.
Wasu manyan misallai a cikin kasafin kudin Fadar Shugaban Kasar, sun hada da Naira biliyan 1.2 na sayen motoci, Naira biliyan 1.1 na kula da jiragen shugaban kasa, Naira biliyan 1 na ginin bangaren shugaban kasa a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da kuma Naira miliyan 500 na gyaran asibitin gidan gwamnati, wanda ya fara aiki a shekarar 2023, a yayin da aka shaida wa ‘yan Nijeriya cewa, asibitin mai matukar inganci ne a duniya; wanda ke tattare da kowace irin na’ura da ake bukata. Ka da dai a manta cewa, wannan asibiti ba na karabiti ba ne. Da irin wannan rashin kishin kasa ka da a yi mamaki idan gogan ya ce; zai je Kasar Faransa a duba lafiyarsa.
Har ila yau, idan aka dubi kasafin kudin da aka rattabawa hannu; kimanin watanni biyu baya, a ciki an ware Naira biliyan 6.9, domin sayo motocin Fadar Shugaban Kasa da kuma ware wani kaso na Naira biliyan 1.5; domin sayo motocin ofishin Uwargidan Shugaban Kasar, wanda a kundin tsarin mulki; ofishin ba shi da wata kima ko wani tanadi a ciki.
Wani abin al’ajabi shi ne, kasafin kudin ya kuma ware wasu kudade domin gyaran wuraren zama na shugaban kasa a kan Naira biliyan 4, gyaran gidan Aguda a kan Naira biliyan 2.5, gyaran gidan shugaban kasa na Dodan Barracks, a kan Naira biliyan 4, gyaran gidan Mataimakin Shugaban Kasa a Legas a kan Naira biliyan 3, kuma fa wannan kudin ranto su za a yi.Ko shakka babu, wannan ya yi kama da rashin hankali da tsantsar wauta.
A karshe
Kasafin kudin ya nuna rashin kishin kasa da hangen nesa. Don haka, ya kamata masu madafun iko su yi karatun ta nutsu.