Jama’a barkanku da kasancewa tare da shafin Taskira, shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al’umma, kama daga fannin zamantakewar rayuwar yau da kullum, rayuwar ma’aurata, rayuwar Matasa (Soyayya), da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da irin matsalolin da ke afkuwa ga wasu matasan Mata, musamman ta yadda wasu iyayen ke bar wa ‘Ya’yansu mata wahalhalun sayen kananun abubuwa da suke bukata na rayuwar yau da kullum wanda ya shafe su.
Wanda sanadiyyar hakan ke sa mafi yawan ‘Yan mata lalacewa, Ko laifin waye tsakanin uwa da uban? Wadanne irin matsaloli hakan ke iya haifarwa?.
Dalilin hakan shafin Taskira ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu, inda suka bayyana ra’ayoyinsu kamar haka:
Sunana Princess Fatimah Mazadu daga Jihar Gombe:
Abun da zan ce gaskiya abun sam! bai dace ba, saboda in ka san ba za ka iya daukar dawainiyar yaranka ba, gwara ka nemi sana’a ko ka nema musu dan dogoro da kai. Laifin na dukkansu ne, uwa nata tarbiyya ce, martaba da nasaba na uba ne, dan haka dukkan laifin nasu ne, ai in uban baiyyi ba ke sai ki nemi sana’a kina yi na gida kina taimaka masa da kulawa da yaran tunda kananun abubuwa aka ce ba wai dukka dawainiyoyin ba. Lalacewa ta fannin Zina, sata, shiga kungiyoyi marasa kan gado, kau da imaninsu daga tausayi iyayensu. Gaskiya na taba, amma su zan ce tsantsar talauci ne, gashi uban baya son su fita sana’a gani yake in sun fita za a yaudari talaucinsu a lalata masa tarbiyyar yaransa. Shawara daya ce su tashi a tsaye kan tarbiyyar yaransu, dan duk sanda baka iya biya wa yaranka kananun abubuwa toh kana kara nisantasu da tarbiyyar da ka tadasu ne daga farko, saboda haka a kiyaye sosai iyaye, sannan ku ‘yan mata in iyayenku basa iya muku wasu kananun abubuwa toh ku danganta da hakuri ku nemi sana’a, ba dole sai ta talla ko ta zubda mutumci ba, dan wani lokaci saye-saye na mata sai iyaye masu hakuri abubuwan da yawa especially in an balaga dinnan. Allah ya shirya mana zuriya, ya bamu ikon kulawa da su bisa tafarkin manzon Allah (S. A. W).
Sunana Amina Mu’awuya Mukhtar:
Bai kamata ba, domin hakan na iya janyo mafi yawancin ‘ya’ya mata rayuwarsu da tarbiyyar su ta lalace, saboda ita mace rauni ne da ita, kuma bayyanar rauninta a inda bai dace ba yana iya bawa mugayen mutane damar cutar da ita. Uba da Uwa duka kowa yana da lefi, amma shi Uba shi ne babban me lefi, domin kuwa shi ne wanda nauyin uwa da kuma ‘ya’yanta ya rataya a kansa, dole ne kuma ya sauke wannan nauyi. Ita kuma uwa laifinta shi ne da ba za ta nunawa ‘ya’yanta cewa ba komai ake nema a samu ba, duk da cewa abu ne wanda za a iya cewa ya zama dole ayi musu, amma duba da yanayi na rayuwa dole uwa ta nunawa ‘ya’yanta akwai da kuma babu, ta yadda za su iya rayuwa a kowanne irin yanayi, tunda su ma watarana iyaye za su zama. Lalacewar tarbiyya da kuma rayuwar ‘ya’yan, ba kuma za su taba jin tausayin Uban nasu ba. Ba kuma za su ga darajar sa ba, yawancinsu ba sa zaman aure ko da sun yi wasunsu ma ba su yin auren, domin gani suke zaman auren takura ne. Kwarai kuwa na taba cin karo da wadda ta fusknci hakan, wadda a halin yanzu ma zaman kanta take yi, kuma uwa da uba duka suna a raye. Shawarar dai ita ce iyaye su ji tsoron Allah, domin yaransu amana ce a gare su, domin Allah zai tambaye su amanar da ya ba su. Sannan kudin ga koaarin daukewa ‘ya’yaku nauyin daya wajaba akanku, sannan a koya musu rayuwa a kowanne irin yanayi na akwai da babu domin suma watarana za su zama uwa. Kuma ‘yan mata ku ji tsoron Allah ka da hakan ya zamo silar lalacewar rayuwarku na har abada, domin kowanne bawa da irin abun da Allah ke jarabtarsa da shi, kaddaranki rubutacciya ce ba za ki taba canjata ba. Allah ya sa mu fi karfin zuciyar mu.
Sunana Musbahu Muhammad daga Gorondutse Jihar Kano:
Ya kamata iyaye su san duk abin da ‘ya’yansu mata ke bukata na yau da kullum, ko na wata-wata, saboda dole sai da wadannan abubuwan rayuwarsu za ta inganta, bar musu wannan abubuwan shi zai sa su tambayi wani mutum wanda daga haka shikkenan an kama hanyar lalacewa. Laifin uba ne dan duk a karkashin kulawarsa suke. Hakan na haifar da lalacewar mata ta bangarori daban-daban. Eh! Na taba cin karo da hakan. Shawarata su iyaye su ji tsoron Allah su kula da amanar da Allah ya ba su, su kuma ‘yan mata su kiyaye kansu daga son rai ko son birgewa. Sannan su kama sana’a komai kankantarta za ta taimaka musu, su mazan da suke amfani da su dan su basu abin da suke bukata, wataran za su guje su, za su juya musu baya.
Sunana Habiba Mustapha Abdullahi Brigade Gama-A, Jihar Kano:
Talauci ne yake kawo haka, iyayen maza da mata Allah ya baku ikon biya mana bukatunmu, Laifin uwa ne. Matsalolin da ka iya haifarwa su ne; Tabarbarewar rayuwa, yawan fyade. Eh! na taba cin karo da me irin wannan matsalar. Shawarata dan Allah iyayenmu su kara kula wajen tarbiyya da shige da fice na yara.
Sunana Aisha Musa Yankara daga Jihar Kano:
To dama indai ba iyayen suka bawa yarinyar sana’ar da za ta dauki dawainiyar wani abin ba ai kun bude kofar lalacewar ta da kanku, wanda kuma hakan sam! bai kamata ba. Dukkansu suna da laifi, amma na uba yafi, dalili kuwa shi ne; idan ita uwa matsayinta na mace ba ta yi tunanin dakatar da ‘yarta aikata wani mummunan abu ba, domin daukar dawaimiyarsu aikai. Uba a karkashin ikonka suke su duka kai ne ya kamata ka tsawatar da su, su dukan ko da kuwa da hadin kan uwar to matukar suna jin maganarka za su bar wannan hanyar da suka dauka Allah ya shirya mana zuri’a. Matsaloli da yawa zai iya haifar wa, misali; fandarewar yarinyar daga zarar ta ga tana daukar nauyinku, maganar ma yi maku biyayya babu ita don gani take ita ke baku karshe ma sai ki ga iyayen ke wa yarinyar biyayya. Ban taba cin karo da irin wannan ba gaskiya. To shawara anan mu jajirce, mu kuma mike idan mun haifa mu dage wajen ganin mun ba su kulawa da tarbiyyar da ya dace, Allah ya dafa mana amen.
Sunana Muhammad Kabir Kamji Batsari, Jihar Katsina:
Alhamdulillah ala kulli halin sanin kowa ne ita ‘ya mace wata aba ce wadda ke son kulawa gami da tarairaya, duk macen da ta rasa hakan za ta iya fadawa wani yanayi na rashin kyautawa, wata kuma za ta yi hakuri a yadda take, amman yin hakan da iyaye suke yi ba karamin kuskure bane. Allah ya sa mu dace. Laifin uwa ya fi yawa a ciki, sabida ta fi uba sannin halin ‘yar ta su, sannan ta fi uba sanin abin da zai kare ita diyar daga fadawa halaka. Matsaloli; kai tsaye wata za ta iya sadaukar da jikinta akan kan wata bukatar ta, wata kuma za ta iya bada kanta don ta mallaki abin da take so (a’uzubillahi). Tabbas! na taba haduwa da wadanda suke cikin kalar wannan masifar. Shawarata anan ita ce duk halin da bawa ya tsinci ikansa, to ya sani akwai Allah, ya sa hakuri a cikin rayuwar sa (innallaha ma’assabirin). Shawarata; Ya ku iyaye ku-kula da diyarku ku rinka jansu a jiki, kuna mai tanbayar su ‘yan bukatunsu ko da ba duka za ku yi masu ba. Ya ku ‘yan matan da ke bada kansu dan abin duniya, Allah ya shiryeku, ki duba wata za ki ga kin fi ta, shin kina tunanin Allah baya sane da ke ne? a’ah Allah yana sane da kowa. Idan kin nemi abu baki samu ba ki yi hakuri, ki jira lokaci ka da ki yi gaggawa.
Sunana Ibraheem Ismail daga Jihar Kano:
To a gaskiya bai dace ba, sabida kuskure ne mai girma, idan iyayenmu kuka ce kun dora musu wasu nauyi akansu ta haka wasu bata garin suke samin damar lalata tarbiyyar da kuka yi shekara da shekaru kuna dawainiya, ta yadda za su amfanar da kansu, amma sabida sa su a wani layi wanda karshensa dana sani ne, Allah ka kiyashe mu da aikata aikin dana sani, kuma masu baiwa wannan yara alhakin yin haka Allah ka ganar da su. Da farko laifin uba ne tunda kai ne ‘driber’ duk wata ‘power’ tana hannunka idan ka wadatar da iyalinka ka nuna musu samu da rashi na Allah ne to haka ba za ta faru ba. Hakan yana haifar da lalacewar zuri a, ba ma iya zuri a ba al umma za a ce. A’a gaskiya ban taba cin karo ba. Shawara ita ce; yin hakan ba dai-dai bane mutukar ana so a gudu tare a tsira tare, kawai abinbda aka samu da dadi ba dadi ayi amfani da shi, sai rayuwa tayi kyau. Su kuma ‘yan matan su ji tsoran ubangiji yayin da kika tsinci kanki a irin wannan halin, duk wuya duk rintsi ki tsare mutuncinki, dan mutunci madara ne, idan ya zube ba shi debuwa, Allah ya sa mu dace.
Sunana Fa’iza Hashim Hassan daga Jihar Jigawa:
Iyaye ya kamata su dauke duk wata dawainiya ta yaransu. Idan suka bar wa yaransu wata bukatar za su bi wata hanya, domin samo mafita a gun da ba ta da kyau. Kowa yana da laifi, uba ne ya kamata ya dauke duk wata dawainiyar iyalinsa. Ita kuma uwa ta zama me kula da abin da ke tare da yaranta. Matsalar hakan kan sa wasu lalacewa kamar bin maza, Mata da dai sauransu. Eh! na taba cin karo sosai. Shawarata shi ne; Iyayen su san da wa yaransu ke mu’amala, ‘Yan mata ku sa su rike mutuncinsu su yi hakuri da yadda rayuwa ta zo musu.
Sunana Mas’ud Saleh Dokadawa:
A gaskiya hakan yana faruwa, kuma sau da yawa yana kawo gurbatar tarbiyyar ‘ya’ya mata, kuma iyaye suna taka rawar gani sosai akan hakan, wannan yana kawo lalacewar tarbiyyar da rayuwar su. Laifin uba ne, saboda hakkinsa ne ya samar da duk wani abu da ake bukata na cikin gida wanda ya zama dole sai an yi amfani da shi. Ita kuma uwa tana samun laifi saboda ‘ya’ya mata ba sa iya tunkarar iyaye maza da bukatunsu na sirri, sai dai su gayawa iyaye mata su fadawa Uba. Sannan kulawar wannan bukatun hakkin uwa ne don ita ke tare da su, koda yaushe, shi Uba hakkinsa shi ne; samar wa ko bada kudin da za a siya. Matsaloli; Ana iya amfani da hakan a taba wasu sassa na jikinta daga samari, saboda tana da bukatar kudi a wajensa. ‘Yan mata sukan koyi roko a wurin samari ko ba komai zubar da mutuncinsu ne. ‘Yan matan suna iya bada kansu ayi lalata da su, don samun kudin biya wa kansu kananun bukatu. Wasu ma matan daga nan suna iya afkawa karuwan gida ko na waje. Na taba cin karo da wacce hakan ya faru da ita, kuma ta shiga halin lalacewar tarbiyyar da mutunci. Shawarwarin sune kamar haka; Iyaye Maza su sawa ransu cewar biyawa ‘ya’ya mata kananun bukatu yana cikin hakkin wajibi. Iyaye mata su rinka sanar da uba bukatun ‘ya’yan don ganin uba ya siyo, ko bada kudin don siyo wa. Sa ido ga iyaye yayin da ‘ya’yansu mata suke samu ko rasa wannan bukatun don gudun fadawa wata hanya da ba dai-dai ba. Su kuma ‘yan matan da hakan ya faru da su, su nemi sana’a ko wani abin yi don tsare mutuncin kansu. Komawa ga Allah da gyara halayensu, tunda sun ga illar hakan a baya, Kiyaye duk wasu abubuwan da za su iya kaisu ga komawa rayuwar baya.
Sunana Maryam Rabi’u daga Jihar Kano karamar hukumar Nassarawa:
Gaskiya hakan bai dace ba, don ‘ya’ya mata suna da bukatu na musamman ta fannin rayuwarsu. Eh! hakan na iya janyo musu shiga wata rayuwa mara kyau, wacca daga baya in ba a yi saurin daukar mataki ba ka iya jefa su cikin wani hali. Za mu iya cewa laifin uwa ne.Yarinya za ta fara rokon samarinta kudi, da makamantan irin haka. gaskiya ban ta’ba cin karoba, sai dai inajin labari. Shawarata anan shi ne; ya kamata uwa mace ta kasance ita ce mafi kusanci da yaranta, toh ta hakane za ta iya gano me yarinyarta take ciki, kuma wacca irin gudummawa za ta bata, na matsalolinta na yau da gobe. Su kuma ‘yan matan su yi hakuri su daina kai matsalolinsu gun samarinsu.