Connect with us

WASANNI

Rashin Ronaldo Ya Sa Real Madrid Sun Zama Abin Tsoro – Dani Alves

Published

on

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta PSG, Dani Alves, dan kasar Brazil ya bayyana cewa yanzu da babu Ronaldo a Real Madrid kungiyar tafi zama abin tsoro saboda yanzu kowanne dan wasa zai iya cin kwallo.

Dani Alves ya bayyana hakane a wata hira da ya yi da manema labarai a shirye shiryen da kungiyarsa take yi na fafata wasa da kungiyar Liberpool a wasan cin kofin gasar zakarun Turai na wannan shekarar.

Albes ya ce, Real Madrid dai Real Madrid ce bata canja ba kuma ‘yan wasanta da aka sani har yanzu suna nan kamar yadda aka sansu idan aka cire Ronaldo wanda ya bar kungiyar zuwa Juventus domin ya ci gaba da cin karensa babu babbaka.

“Ni a yanzu nafi ganin Real Madrid za ta fi kowanne lokaci zama mai hatsari saboda a lokacin baya Ronaldo kowa yake tsoro kuma idan aka yi nasara ana iya hanashi yin kokari a wasa amma yanzu babu wanda zaka rike ka hana kungiyar kokari” in ji Dani Alves

Ya ci gaba da cewa, kowanne dan wasa yanzu zai iya zura kwallo a raga kuma su kansu ‘yan wasan kungiyar yanzu sunfi mayar da hankali saboda yanzu sun san babu Ronaldo saboda haka dole sai sun sake dagewa”

A karshe ya ce bai ga laifin Ronaldo ba idan yabar kungiyar ya koma Juventus saboda kowanne dan wasa yana son sabon yanayi kuma shi ma haka ya bar Barcelona ya koma wata kungiyar saboda yana son ya gwada nasararsa a wani wajen.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: