Gwamnatin jihar Katsina ta ce za ta fara bai wa malaman Masallatan Juma’a da mataimakansu da masu unguwanni alawus-alawus domin karfafa musu gwiwa wajen yaki da rashin tsaro.
Gwamna Dikko Radda ne ya bayyana hakan bayan kaddamar da kwamitocin gudanarwa na kungiyar Katsina Community Watch Corps (KCSWC).
- NFF Ta Sanar Da Ranar Fara Gasar ‘Federation Cup’ Ta Nijeriya
- Gwamnan Zamfara Zai Binciki Badakalar Miliyan 774 A Hukumar Alhazai Ta Jihar
A wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Ibrahim Kaula-Mohammed ya fitar, ya ruwaito Radda na cewa kwamitin zai hada kai da sauran jami’an tsaro wajen zakulo ‘yan bindiga a fadin jihar.
Ya ce mambobin kwamitin gudanarwa na kowace karamar hukuma 34 sun hada da kansila, hakimin gunduma, jami’in ‘yansanda na shiyya da wakilan hukumomin tsaro daban-daban.
Sannan ya ce akwai wakilai biyu na ‘yan kasuwa da kuma wakilan kungiyoyin addini.
Gwamnan ya ce kwamitin zai sa ido tare da tantance ayyukan KCSWC a yankunansu tare da gabatar da rahoton wata-wata ga kwamishinan tsaron cikin gida na jihar.
Tun da fari, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Dakta Nasiru Mu’azu-Danmusa, ya bayyana cewa sannu a hankali rashin tsaro na raguwa a fadin jihar tun da aka kafa KCSWC.
A nasu jawabin wakilan mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Aminu Nuhu Abdulkadir da mai shari’a Saddik Abdullahi Mahuta (mai ritaya), sun yaba wa gwamnan bisa daukar matakan magance matsalar rashin tsaro a jihar.
Abdulkadir, wanda shi ne hakimin Rimi da Abdullahi Mahuta, hakimin Malumfashi, sun yi alkawarin ci gaba da bai wa kwamitin goyon baya.