Connect with us

RAHOTANNI

Rasuwar Shugaban Harka Airline Ta Girgiza Jama’a

Published

on

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka bayar da sanarwar rasuwar shugaban kamfanin sifirin jiragen sama na Harka Air Line,SKuadaran Leader Uba Salisu Mohammad mai ritaya,wanda ta girgiza al’umma musamman ‘yan’uwa da abokan arziki, waDanda suka yi babban rashin mataimaki ta fuskar rayuwarsu.

Marigayi Uba Salisu Ibrahim,ya rasu a gidansa da ke cikin GRA a Sabongarin Zariya, bayan ‘yar gajetuwar rashin lafiya.

Wakilinmu ya samu zanta wa da Barista Maryam Salish da ke aiki da maaikatar shari’a  Zariya, kuma babbar ya ga marigayin.

Ta kuma shaida wa wakilinmu cewa,marigayin ya yi ‘yar gajeruwar rashin lafiya a ranar Asabar, inda Allah ya Dauki rayuwarsa  ranar Lahadi a wani Asibiti a Kaduna

Ta Kara da cewa, ranar da ya rasu yake cika shekara Sittin a duniya, ya bar mata biyu da ‘ya’ya bakwai, kuma tuni dai aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Mususulinci ya tanada a gidansa da ke GRA Zariya. Daruruwan jama’a ne da kowane sashi suka halarci wajen jana’izar, wanda kuma suka yi ta nuna alhininsu bias wannan rasuwa tare kuma da yi masa addu’ar neman gafara daga Allah.

Mutane da yawa sun bayyana kyawawan halin marigayin ta fuskar taimako da tausayawa al’umma da sada zumunci da kuma sakin fuska ga jama’a.

Shi kuwa Daya daga cikin aminan marigayin, Aminu Maude ya bayyana cewa,sun haDu da shi tun suna Dalibai a makarantar horon yara sojoji wato Nigeria Military School kimanin shekara arbain da biyar da suka gabata har zuwa ranar da ya rasu a matsayin ‘yan’uwa kuma abokai suke.

Ya ci gaba da cewa,daga cikin halayarsa akwai taimako, da son zumunci da riKon amana da girmama aKidun jama’a tare da tallafa wa marasa galihu a cikin al’umma

Burgediya Aminu Maude,ya ce za su dade ba su manta da irin halayar marigayin ba, a don haka ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa.

 

A Karshe ya shawarci iyalin marigayin da su Dauki rashin, a matsayi tsari daga Allah cewa dukkan mai rai zai DanDana mutuwa, kuma ba za su yi Kasa a Kwiwa ba wajen ci gaba da tallafa wa iyalin marigayin.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: