Jarumar Kannywood, Hadiza Gabon, ta shaidawa wata kotun shari’a dake zamanta a Kaduna cewa rayuwarta na cikin hadari.
Wani ma’aikacin gwamnati Bala Musa ne ya kai ta kotu bisa zargin kin aurensa bayan ya kashe mata zuzurutun kudi har Naira 396,000.
Jarumar dai a zaman kotun da ta gabata ta ce sam ba ta san Wani Malam Bala Musa ba (mai korafin).
Da take jawabi a kotun ayau Litinin, wadda ake zargin ta bakin lauyanta, Barista Mubarak Sani Jibril, ta ce da tabarbarewar tsaro a kasar nan, jarumar tana tsoron kare lafiyarta.
A cewarsa, suna cikin damuwa a kullum suka tuna da batun shari’ar, kasancewar ita (Gabon) ta kan fita daga kotun ne duk lokacin shari’ar a fakaice.
“Kula da rayuwa ta yana da mahimmanci sosai kamar yadda kula da rayuwar sauran mahalarta dakin shari’ar ma ke da amfani.
“Rayuwa ta (Lauya) tana cikin hadari, rayuwarta (Gabon) na cikin hadari, shi ma rayuwar shi (mai korafin) na cikin hadari.
“Ba mu san wadanda suke tare damu a wannan dakin shari’ar ba daga shafukan sada zumunta ba.
“Abu na gaba da za ku fara ji, shine ganin mutane da bindigogi a nan don yin garkuwa da mu. Wannan shi ne abin da ke damunmu ba shari’ar da ake yi a kotun ba,” inji lauyan Gabon.