An dade ana noman citta a kasar nan, musaman Arewacin Nijeriya, ganin yadda noman ke samar wa manonanta kudi masu yawa.
A jihar Sakkwato da Zamfara da Jigawa da Kano da Katsina da Kudancin Kaduna, ana zuwa domin siyenta.
karamar hukumar Kaciya da Kagarko da Kubaca da ke cikin karamar hukumar Kagarko da Barde da Fori da ke karamar hukumar Jama’a, sai Kwoi da ke karamar hukumar Jaba, su ne manyan garuruwan da ke samar da kaso ma fi yawa na citta.
Wadannan yakunun, a daukacin fadin kasar nan inda nan ana zuwa siyenta, inda wasu kuma ke zuwa garin Kafancan domin siyenta.
Rahotannin sun bayyana cewa, a duk mako, tireloli 15 zuwa fiye da haka ke jigilarta daga Kafancan, inda a kowace jigila daya, ake dakon tan daga 26 zuwa 28.
Bugu da kari, nomanta da kasuwancinta da gyaranta na daga cikin harkoki ma fi girma da ke bunkasa harkokin arziki da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al’ummar Kudancin Kaduna.
Cittar da ake noma wa a Kudancin Kaduna, wadda kuma aka yi amanna tana daga cikin ma fi kyau a duniya, a kan fara dibanta daga watan Nuwamba zuwa watan Afirilun.
A lokacin da ake ganiyar aikin cittar, mutane da yawa da suka hada da manya da kananan ’yan kasuwa da dillalai da direbobi da masu dako da masu gadi da masu aikin tsinta da shika da gyaran cittar, kowane kan kama aiki gadan-gadan, baya ga manomanta da ke fito wa da ita domin siyarwa a kasuwa.
Haka kuma, matasa na daga cikin wadanda ke cin gajiyar aikinta a karamar hukumar Jama’a da kuma garin Kaciya.
Sannan,haifaffun garuruwan, akwai masu aikin cittar da musamman suke baro garuruwansu su taho yankin don aikin gyaranta a kowace shekara.
Rahotannin sun ci gaba da cewa, lokacin da gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin a garkame iyakokin Nijerya, an ci gabna da jigilarta daga Nijeriya zuwa ketare kamar irin su, kasashen Benin da Ghana da Togo.
Sai dai, masu harkar cittar zuwa wannan yanki sun tabka asara a daidai lokacin da kasar ta rufe iyakokinta, inda hakan ya rutsa da tarin manyan motoci dauke da danyarta.
An ruwaito wata mata mai suna Jummai Jacob da ta dade tana sana’ar gyaranta a garin Kaciya ta bayyana cewa, ta fara aikin gyaranta ne a 2016.
Jummai ta ce ta fara gyaranta ne da buhu hudu a ranar farko amma a yanzu ina iya gyara buhu 30, inda ake biyanmu naira 100 a kan kowane buhu.
Jummai ta ce, da wannan aikin ne take daukar nauyin hidamar iyayenta da kula da karatun ’ya’yanta biyu.
Shi kuwa wani Sani Baba ya ce, ya kwashe fiye da shekara ashirin yana aikin cittar, inda ya kara da cewa, tun lokacin da ake biyansu naira 15 zuwa 20 a kowane buhu.
Ya kara da cewa, da aikin ne yake kula iyayensa da karatunsu, inda ya kara da cewa, aikin buhu 40 a kowace rana amma yanzu saboda leburori sun yi yawa ciki har da matan aure, hakan ya sa buhu 25 kawai take samu.
Shi ma wani mai aikin Malam Abdullahi, ya ce ya shafe shekara hudu yana sana’ar siyan da buhunan citta bayan an tsince manya da kanana an tankade ta, sai a saya domin sayar wa ’yankoli.
Ya ce da wannan aikin yake daukar nauyin karatun ’ya’yansa da kuma yin dawainiyar gidansa.
Shi kuma wani matashi da yake yin aikin Sani Musa ya bayyana cewa, da kudin da yake samu na aikin gyranta ne yake taimaka wa kansa da kuma iyayensa, inda ya ci gaba da cewa, ya fara zuwa aikin ne tun ina dan shekara 11, inda yake samun daga naira 200 zuwa naira 500.