Magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a Jihar Ribas, sun sake kalubalantar gwamnan jihar, Nyesom Ezenwo Wike, inda suka ce sun fi shi biyayya ga jam’iyyar.
Da yake jawabi yayin taron kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a Fatakwal, babban daraktan kwamitin a jihar, Dakta Abiye Sekibo, ya ce yawancin wadanda aka hana tikitin takarar gwamna a jihar, ba su fice daga jam’iyyar ba kuma ba su watse ba.
- Adeleke Ya Dakatar Da Lasisin Masu Hakar Ma’adinai A Osun
- Shugaban Afirka Ta Kudu Ya Tsallake Rijiya Da Baya Kan Shirin Tsige Shi
Sekibo ya ce: “Idan har an hana mu tikitin zama gwamna, kuma har yanzu muna tallafawa jam’iyyar da dukkan karfinmu, to mu ’yan jam’iyya ne, to shi fa, me ya yi tun bayan faduwa zaben fidda gwani na jam’iyyar?
“Don haka mu ’yan jam’iyya ne, kuma mun fi mara mata baya. Wannan shi ne abin da ya bambanta mu da shi”
Shi ma da yake jawabi, shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Sanata Lee Maeba, ya ce masu goyon bayan muradin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar sun shafe shekaru da dama suna jam’iyyar.
Maeba ta ce: “A nan na san kun gamsu cewa girman mutanen da ke wannan teburin ya yi daidai da sunan PDP.
“Wadannan mutane gaba daya PDP a cikin jininsu take.
“Don haka muna kira ga mahukuntan jihar kan hare-haren da ake kai wa mambobinmu bai dace ba.”
Tsohon dan majalisar wanda ya bayyana takaicinsa kan yadda Wike ya ki yin Allah wadai da harin da aka kai masa a gidansa da ke Fatakwal kwanan nan, ya ce babu amfanin saka ‘yan daba a siyasar jihar.
Ya ce: “Kuna iya ganin al’amuran rashin tsaro da yawa a nan; ‘yan daba, tashin hankali, ba abu ne da zai amfani kowa ba.”