Dan wasan kwallon kafar Tunisia Nizar Issaoui ya mutu sakamakon kunar da ya samu a lokacin wata zanga-zangar adawa da rashin adalcin ‘yan sanda, kamar yadda iyalinsa suka bayyana, lamarin da ya sa ya cinna wa kansa wuta.
Tun da farko dai an hango Issaoui cikin wani bidiyo da aka wallafa a intanet inda a ciki yake ihu cewa dan sanda sun zarge shi da ta’addanci bayan wata rashin jituwa tsakaninsa da wani mai sayar da kayan marmari.
- Yadda Uwargida Za Ta Yi Kwalliyar Gida Da Sallah
- Buhari Ya Dakatar Da Kwamishinan Zaben Jihar Adamawa
A wani sako na daban, ya ce ya yanke wa kansa hukuncin kisa ta hanyar wuta sai dai an samu kaurewar arangama a wajen jana’izar matashin mai shekara 35 ranar Juma’a a kauyensa Haffouz, kamar yadda kafafen yada labarai suka sanar.
Dan sanda sun zargi Issaoui da aikata ta’addanci bayan da ya yi korafin cewa bai iya siyan ayaba kan kasa da dinare 10 ba kan kilo daya, ninki biyu na farashin da gwamnati ta saka, a cewar rahotanni.
A wani sakon Facebook, dan kwallon ya rubuta saboda sabani da wani mai sayar da ayaba kan dinare 10, ‘yan sanda suka zarge shi da ta’addanci saboda yin korafi a kan ayaba. An samu tashin hankali a jana’izar dan wasan yayin da masu zanga-zanga
suka rika jefa wa ‘yan sanda duwatsu ya yin da su kuma jami’an suke watsa musu hayaki mai sa hawaye.
Tsohon dan wasan kungiyar US Monastir ta kasar Tunisia ne, kuma mahaifi ga ‘ya’ya hudu sannan dan uwansa ya fada wa ‘yan jarida cewa Issauoi ya kone sosai kuma likitoci ba su iya yin wani abu na ceto rayuwarsa ba.
Matakin da ya dauka ya yi daidai da wata zanga-zanga da aka yi a 2010 lokacin da wani mai siyar da kaya a bakin titi Mohamed Bouazizi ya cinna wa kansa wuta lamarin ya janyo zanga-zanga da ta kai ga hambarar da Shugaba Zine al-Abidine Ben Ali.
Shugaba Kais Saied mai ci, ya janyo ce-ce-ku-ce a 2021 lokacin da ya kori firaminista tare da dakatar da majalisar dokokin kasar kuma tun daga lokacin ya yi amfani da sabon kundin tsarin mulki wanda ya tabbatar da ikonsa.