‘Yan majalisar wakilai biyu daga jihar Kano, wadanda ke wakiltar jam’iyyar NNPP, sun bayyana ficewa daga tafiyar Kwankwasiyya karkashin jagorancin tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
‘Yan majalisar wakilai biyu da suka hada da Aliyu Sani Madakin Gini, mai wakiltar Kano Municipal da Alhassan Rurum (Rano/Kibiya/Bunkure) sun tabbatar da cewa ba za su ci gaba da tafiyar Kwankwasiyya ba, lamarin da ke nuna cewa rikicin jam’iyyar NNPP a Kano ya kara kazancewa a halin yanzu.
- Tinubu Ya Taya Trump Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Amurka
- Shugaba Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Bude Taron Kasa Da Kasa Game Da Tsaffin Al’adun Wayewar Kan Al’umma
Rurum, wanda tsohon shugaban majalisar dokokin Jihar Kano ne ya bayyana ficewarsa daga Kwankwasiyya a wata gajeriyar tattaunawa ta wayar tarho da jaridar Daily Trust.
Duk da dai bai bayar da wasu takamaiman dalilan da ya sa ya yanke wannan shawarar ba kafin karshen wayar, ana ganin ficewar Rurum na da alaka da rikicin da ya barke a baya-bayan nan da gwamnatin Jihar Kano karkashin jam’iyyar NNPP, musamman biyo bayan rusa masarautun biyar da gwamnatin ta yi.
Matakin dai ya shafi Rurum ne kai tsaye, domin yana rike da sarautar gargajiya ta Turakin Rano a cikin masarautar Rano da aka rushe a yanzu.
A nasa bangaren, Madakin Gini wanda shi ne mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai ya fito fili ya nisanta kansa daga Kwankwasiyya yayin da yake jawabi ga al’ummar mazabarsa a Kano ranar Lahadi.
“Daga yau, ni Aliyu Sani Madaki, ba ni da wata alaka da tafiyar Kwankwasiyya.
“Sun kore mu, sun ce ba mu da goyon baya, amma ba ma tsoron mu tsaya mu kadai. Su sani, babu wanda ba zan iya tinkara ba a tafiyar Kwankwasiyya daga sama har kasa, idan akwai bukatar hakan,” in ji shi.
Ya soki kungiyar Kwankwasiyya, wanda aka fi sani da alamar jajayen hula, dangane da yadda take tafiyar da jagorancinta.
Madaki Gini ya ce, “Wannan kungiya ta Kwankwasiyya, idan ya kasance kamar addini ce, to mun biya man biya hakkinmu. Amma sun ce ba mu da amfani, cewa ba mu da goyon bayan al’umma. Ya kamata su gane cewa babu wani a cikin Kwankwasiyya da ba zan iya fuskantarsa ba kai tsaye.”
A wani sako kai tsaye da ya aike wa magoya bayansa, Madakin Gini ya bukace su da su yi watsi da jar hula, inda ya kira hakan alama ce ta mika wuya da ya daina amincewa da ita. “Daga yanzu duk wanda ya dauke ni shugabansa a siyasa, to ya cire jar hula. Mata su cire jajayen mayafi. Mun gama!”
Da yake jawabi kan gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, Madakin Gini ya bayyana damuwarsa kan yadda gwamnan ke fuskantar matsin lamba a cikin tafiyar Kwankwasiyya.
Ya ce, “Sakona ga gwamna a fili yake. Suna kokarin raunata shi. Ina kira a gare shi ya tsaya da kafafuwansa, in ba haka ba, yana iya ruftawa. Ina da basira game da tsare-tsare a kansa.”
Idan dai za a iya tunawa a kwanakin baya ne wata kungiya ta fara wani yunkuri na neman gwamnan ya tsaya da kafafuwansa, ya daina daukar umurni daga wurin uban gidansa jagoran tafiyar Kwankwasiyya, wanda suka yi zargin cewa shi ke juya gwamnan wurin harkokin yau da kullum na gwamnati.
Haka zalika, rikicin da ke cikin jam’iyyar NNPP mai mulki a Kano na neman kazancewa, inda gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya fara kin daga wayar mai gidansa Rabi’u Musa Kwankwaso, sannan ya ki halartar tarukan da jagoran NNPP na kasa ya shirya.
Da alama dai wannan taken na “Abba tsaya da kafarka” ya fara tasiri a gurin gwamnan bayan da wasu ke ta motsa yadda zai karbe iko da jam’iyyar da kuma Kwankwasiyya daga hannun Kwankwaso.
Wasu majiyoyi sun shaida cewa tuni Abba ya fara amsa kira bayan da aka nusar da shi cewa Kwankwaso ne ke juya gwamnatinsa, inda kusan kashi 90 na makaman da Abba ya yi daga bangaren Kwankwaso ne.
Majiyoyi sun bayyana cewa Abba ba ya jin dadin karfa-karfa da Kwankwaso yake yi masa, inda ya fara nuna alamun bore domin ci gabansa na siyasa da ma Jihar Kano baki daya.
Tun lokacin da aka ga gwamnan a bikin murnar zagayowar haihuwar Kwankwaso, har yanzu ba su sake haduwa ba. Majiyoyi sun bayyana cewa duk tarukan da Kwankwaso ya kira a Kano da Abuja, Abba bai halarta ba.
Majiyoyin sun kkara da cewa har Abuja Kwankwaso ya bi gwamnan, amma Abba bai bari sun hadu ba, kuma har dan aike ya tura masa amma ya ki ganuwa a wajen Kwankwaso.
“Yanzu haka ana shirin hada kai da wasu ‘yan APC da ‘yan kungiyar Abba tsaya da kafarka wajen samo umarnin kotu da zai kori dukka wadannan ciyamomin da aka rantsar, sai dai a bai wa tsagin da Mai Shari’a Simon Amobeda ya tabbatar ana gobe zabe,” in ji majiyar.