Rikicin Shugabanci A Kungiyar Kwadago Ta Karamar Hukumar Kudan Na Kara Zafi

Daga  Idris Umar, Zariya

A makon da ya gabata ne jaridar LEADERSHIP A Yau ta yi kacibus da wata kura da ta turnuke shugabancin kungiyar kwadago na karamar hukumar Kudan a jihar Kaduna.

Hakan ya sa wakilinmu ya garzaya don zakulo wa masu karatu cikakken abin dake faruwa.

Da farko dai akwai tabbacin cewa tataburzan dake faruwa a wannan kungiya ta samo asali ne akan yadda shugabancin kungiyar ya zama abin wasa.

Kwamared Garba Ibrahim shi ne shugaban kugiyar ta kwadago reshen karamar hukumar ta Kudan to shekarunsa na ritaya sun cika kuma har ya aje aikin nasa to bisa yadda dokar kasa ta tanada a duk lokacin da ba shugaba to maitaimakinsa ne zai tsaya a matsayin sa, to a wannan kungiya sai aka semi akasin hakan Inda bincike ya nuna cewa shugaba mai tafiya maimakon ya dankawa mataimakinsa ragamar shugancin to sai ya janyo sakatarensa mai suna malam Lukman Dallami ya danka masa ragamar shugabancin kungiyar da zai tafi shi kuma mataimakin nasa ko oho.

Kwamared Yahaya Sa’idu Hunkuyi, shine mataimakin shugaba da doka tace abashi akalar kungiyar wanda ganin irin wacan hukuncin da shugaba mai barin gado ya zartar hakan yasa shima yaja daga da wasu ‘yayan kungiyar tare da nuna cewa atafau dole ne abi doka kamar yadda yake a kundin tsarin mulki kasa.

Hakan yasa jaridar Leardership A Yau tayi kokarin jin ta baki kowane daga cike masu fada aji na daga cikin kungiyar.

Shi Kwamared Yahay Sa’id mai rike da kujeran mataimakin shugaba a da Kuma mai ikirarin shine shugaba a yanzu ya Nuna cewa,sam bazai yiwuba su amince da keta dokar kungiyar tasu ba kuma ya janyo hankalin iyayen kungiyar ta jihar kaduna cewa suyi watsi da aniyar sakataren kungiyar tasu na cewa shine shugaba kungiyar,yace lallai su a sakatare suka sanshi kuma basu koreshiba amma dai kujeran shugabanci a yanzu ya hakura da ita doka ta baiwa mataimakin tsohon shugaba ne.

Kwamared Yahaya ya kara da cewa yanzu shi a matsayinsa na shugaba yana kira ga ‘yayan kungiyar da suyi watsi da duk wani jitajita dake kokarin raba kawunan su kuma yayi alkarin zai share masu hawayen su kamar yadda doka ta tanada yace,da yaddar Allah kwaliya zata biya kudin sabulu.

Jaridar LEADERSHIP A yau ta nemi jin ta bakin sakatare  malam Lukuman Dallami mai kalubalantar mataimakin shugaban akan kokarinsa na son ya zama shugaban kungiyar mai kuma ikirarin shine shugaba tunda shugaban yayi ritaya ta water salula amma yace zai magana ya zuwa hada wanan labarin LEADERSHIP A yau ta gaza ganinsa.

Wani binciken da jaridar LEADERSHIP ta gudanar ya nuna cewa shi tsohon shugaban kungiyar ta kwadago Kwamared Garba Ibrahim ya baiwa Sakataren nasa damar darewa kujeransa ne bisa abubuwa guda biyu,na farko sunce shugaban kugiyar kwadago na jihar kaduna abokinsa ne shi kuma sakataren sa kanin shugabane na jihar baki daya wato anyi ‘yar gida ne wanda su kuma mutane idansu ya waye suka nuna kin amincewar su.

Amma ya zuwa hada wannan labarin dukkan bangarorin biyu kowa na kallon Kansa ne a matsayin shugaba tare da yiwa juna kallon hadarin kaji.

 

Exit mobile version