• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rikicin Shugabanci Na Barazana Ga Babban Taron Jam’iyyar PDP

by Yusuf Shuaibu and Sulaiman
9 months ago
PDP

Rikicin shugabancin da ya kunno kai a cikin jam’iyyar PDP ya sanya shakku kan ko za a gudanar da babban taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar na kasa, wanda aka shirya zai gudana a watan Fabrairun 2025.

Duk da tabbacin da sakataren jam’iyyar na kasa, Sam Anyanwu, ya bayar na cewa taron zai gudana kamar yadda aka tsara, rarrabuwar kawuna a cikin kwamitin gudanarwa na kasa da kalubalen shari’a na ci gaba da kawo cikas.

  • Fatara Da Talauci Na Yi Wa ‘Yan Nijeriya Miliyan 13 Barazanar Fadawa Kangin Talauci A 2025 — Rahoto
  • Gwamnatin Katsina Ta Fitar Da Naira Miliyan Dubu 50 Domin Samar Da Ruwan Sha 

Anyanwu, wanda a halin yanzu Sunday Ude-Okoye ke ikirarin shi ne halartaccen sakataren jam’iyyar PDP na kasa da kotun daukaka kara ta shaidawa.

Babban taron wanda tun farko aka tsara za a gudanar a watan Oktoba na 2024, daga baya kuma aka kai shi zuwa Nuwamba 2024 kafin a dage shi har gaba daya, ana ganin yana da matukar muhimmanci wajen magance muhimman batutuwan da suka shafi jam’iyyar. Wadannan sun hada da duba tsarin shugabanci, warware rikice-rikicen cikin gida, da tsara dabarun zabe mai zuwa.

A tsakiyar rikicin shugabancin akwai shugaban riko na kasa, Umar Damagum, wanda matsayinsa ya haifar da cece-kuce, wanda ake ta kiraye-kirayen ya yi murabus, musamman daga kungiyar gwamnonin PDP na kara ta’azzara lamarin bisa zargin rashin dinke barakar da ke kara kunno kai a cikin jam’iyyar.

LABARAI MASU NASABA

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

An yi kokarin cire Damagum ta hanyoyin siyasa, ciki har da yiwuwar nada sabon shugaba daga yankin arewa ta tsakiya, amma hakan ya ci tura.

Gwagwarmayar bangaranci dai ta kara dagula al’amuran cikin gida na jam’iyyar, inda aka samu bangaren masu biyayya ga fitattun mutane irin su tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Wadannan rarrabuwar kawuna sun gaza samar da fahimtar juna, wadanda suka zama kalubalen da ya haifar da dakatarwar wasu daga cikin jami’an jam’iyyar.

Yayin da watan Fabrairun 2025 ke gabatowa, masu ruwa da tsaki sun nuna damuwarsu na cewa PDP na fuskantar babban kalubale a gabanta.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta
Tambarin Dimokuradiyya

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

October 17, 2025
peter
Tambarin Dimokuradiyya

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

October 17, 2025
peter
Tambarin Dimokuradiyya

Peter Obi Ya Bukaci INEC Ta Tabbatar Da Shaidar Karatun Dan Takara Kafin Shiga Zabe

October 10, 2025
Next Post
buhari

‘Yan Adawa Sun Caccaki Buhari Kan Kalamunsa Na Cewa, ‘Allah Ne Kadai Zai Iya Gyara Nijeriya’

LABARAI MASU NASABA

gaza

Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba

October 28, 2025
Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

October 28, 2025
Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi

Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi

October 28, 2025
Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

October 28, 2025
An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

October 28, 2025
’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

October 28, 2025
Mutum 18 Sun Mutu, 40 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Kebbi 

An Kashe Mutum 10 A Harin Ramuwar Gayya A Jihar Kebbi

October 28, 2025
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu

October 28, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

October 28, 2025
PDP

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.