Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bai wa daliban jihar su 16 da suka kammala karatun aikin jinya a jami’ar Sudan ta ƙasa da ƙasa nan take.
A ranar Alhamis ne Gwamna Lawal ya miƙa wa ɗaliban Jihar Zamfara da suka kammala karatun aikin jinya takardar shaidarsu daga jami’ar Sudan a gidan gwamnati da ke Gusau.
- Gwamnati Ta Kara Yawan Kudaden Shiga Da Ake Bukatar FIRS Ta Tara A 2025
- Bullar Cutar Da Ke Lalata Citta Ta Sa Farashinta Ya Sake Karuwa A Karo Na Shida
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta bayyana cewa an kwashe ɗalibai 66 da gwamnatin jihar Zamfara ta ɗauki nauyin karatunsu daga ƙasar Sudan a shekarar 2023 sakamakon rikicin da ake fama da shi a ƙasar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, 16 daga cikin 66 da aka kora ɗalibai ne na aikin jinya waɗanda suka kasa yin jarrabawar ƙarshe kafin a fara yaƙin.
“A watan Satumbar 2023, Gwamna Dauda Lawal ya ɗauki matakin jin ƙai don taimakawa ɗaliban Zamfara 66 da aka kwashe daga Sudan.
“A bisa umarnin gwamna, kwamishinan ilimi na jihar Zamfara ya haɗa hannu da mahukuntan jami’ar Sudan domin gudanar da jarrabawar ɗalibai 16 na shekarar ƙarshe, wanda aka gudanar a Nijeriya.
“Jami’ar ƙasa da ƙasa ta Sudan ta aike da takardar shaidar kammala jarrabawar ɗaliban jami’ar jinya 16 da gwamna ya ba su.
A yayin gabatar da takardar shaidar, Gwamna Lawal ya ƙara wa ɗaliban da suka kammala karatun kwarin gwiwar zama jakadu nagari a Zamfara da kuma shiga ayyukan gwamnati na ceto jihar.
“Gwamnatina ta kafa dokar ta-baci a fannin ilimi, inda ta magance matsalolin da ke addabar jihar Zamfara. A halin yanzu muna samun ci gaba mai ma’ana kuma za mu zage damtse wajen saka jari mai yawa a cikin ilimi yayin da yake zama tushen ingantacciyar al’umma.
“Kwamishinan ya bayyana abubuwan da muka fuskanta kafin kammala karatun ku. Muna alfahari da ku.
“Muna ginawa da gyara asibitoci a duk faɗin jihar, amma ba a nan gizo ke saƙa ba. Ba zai yiwu a yi gine-gine ba tare da aikin da ake buƙata ba, don haka kun zo a lokacin da ya dace.
“Kun bi wannan fanni mai ɗimbin fa’ida na aikin jinya, kuma a sakamakon haka, za a ba ku aiki kai tsaye daga gwamnatin jihar Zamfara. Shugaban ma’aikata zai tabbatar da samun aikin ku a gwamnatin Zamfara a hukumance. Ina taya ku murna.”