Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa mutum sama da 800,000 ka iya tserewa daga Sudan sakamon kazamin fadan da ake yi tsakanin bangarorin soji biyu da ke gaba da juna.
Ana ci gaba da gwabza fada a Khartoum babban birnin kasar duk da alkawarin dakatar da bude wuta tsakanin bangarorin biyu.
Tuni dubban ‘yan kasar da ma suka fice daga kasar ta gabashin Afirka.
Kazamin fadan wanda ya barke tun sama da mako biyu da ya gabata tuni daman ya riga ya haifar da kwararar dubban ‘yan kasar ta Sudan zuwa kasashe makwabta da suka hada da Masar da Chadi da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.
Haka suma ‘yan kasashen waje gwamnatocin kasashensu da sauran hukumomi na ci gaba da kokarin kwashe su daga kasar, inda tuni suma dubbai suka fice.
A wani taron manema labarai kakakin ma’aikatar harkokin kasashen waje ta Amurka Bedant Patel, ya ce Amurkawa sama da 700 da ‘yan wasu kasashen aka kwashe ta tashar jirgin ruwa da ke garin Port Sudan a cikin kwana ukun da suka gabata, inda yawan Amurkawan da ake fitarwa daga kasar ya karu tun lokacin da aka fara rikicin.
Ya ce; ”A kokarin hadaka na kasashe, gwamnatin Amurka da hadin gwiwar kawayenta da abokan hadin gwiwa ta fitar da ‘yan Amurka sama da 1,000 daga Sudan tun lokacin da aka fara tashin hankalin.”
Sai dai wasu Amurkawa ‘yan asalin kasar ta Sudan a tashar jirgin ruwa ta Port Sudan da ke jiran a kwashe su sun ce suna nan zaune zaman jiran da ba su san takamaimai halin da ake ciki ba game da shirin tserad da su ba.
Suna kokawa da rashin samun wasu cikakkun bayanai daga hukumomi, inda har ta kai suna sayen abinci da ruwan sha da kudadensu a cewarsu.
Wani daga cikinsu ya ce kusan sa’a biyar suna zaman jiran tsammani babu wani bayani illa dai tun da farko an ce musu su yi hakuri.
Mohamed Madany ya ce shi bai ma sani ba ta jirgin ruwa za a kwashe su ko ta jirgin sama ba shi da masaniyar lokacin da zai bar wannan wuri.
Ya ce kusan kwana biyu bai ko runtsa ba, halin da suke ciki na da tsanani amma duk da haka sun jure.
Rikicin da ya shiga mako na uku, a tsakanin rundunar sojin kasar bisa jagorancin shugaban mulkin soja Janar Abdel Fattah al-Burhan da jagoran dakarun kar-ta-kwana na Rapid Support Forces, ko RSF, Janar Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, na ci gaba da tsananta a sassan kasar daban-daban.
A babban birnin kasar Khartoum ya fi tsanani a babban filin jirgin sama na kasar da fadar shugaban kasa da kuma shelkwatar sojoji.
Fadan da ya barke ranar 15 ga watan Afirilu da ya kare zuwa yanzu a kiyasin hukumomi ya hallaka mutum sama da 600, da jikkata sama da 5000.
Na ga manyan motocin dakon kaya makare da gawarwaki A Yankin Darfur
Fada yana ci gaba da kamari a yankin Darfur da ke Yammacin Sudan, duk da tsagaita wutar da aka yi, inda Larabawa masu gwagwarmaya da makamai ke kai hari a kan manyan dakunan ajiyar kayayyaki, da kasuwanni da gidaje.
An kashe wani babban jami’in ‘yan sanda kuma wani ma’aikacin agaji dan kasar Sudan ya shaida wa BBC cewa yana nan boye a karkashin gado saboda tashin hankalin da ke faruwa.
“Ko ban-daki ba na iya yunkurawa na je,” cewar Abdallalateif ta wayar tarho daga birnin El Geneina.
Wutar rikici ta riga ta ruru inda ta haddasa zaman dar-dar na kabilanci, kamar yadda ya yi bayani.
Shekara da shekaru Darfur tana fama da tashin hankali tsakanin al’umominta daban-daban na Afirka da Larabawa.
A lokacin da wadanda ba Larabawa ba suka dauki makamai suna fada da gwamnati cikin shekara ta 2003, suna korafin cewa ana nuna musu wariya.
Gwamnati ta mayar da martani ta hanyar daukar mafiya yawa Larabawa ‘yan bindiga, wadanda aka zarga da ta’asa da cin zarafi da tursasawa.
Har zuwa zancen da muke yi da ku a yanzu, kungiyoyin ‘yan Afirka da dama da ke yankin Darfur suna zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira don tsira da ransu.
A yanzu Larabawa masu dauke makamai da ke da alaka dakarun kai daukin gaggawa na RSF, wato jami’an tsaro masu kayan sarki da ke artabu da sojoji ga alamu suna amfani da gibin tsaro da ake da shi.
“Na ga manyan motocin dakon kaya makare da gawawwakin mutane, sannan Larabawa dauke da makamai, suna rike da bindigogi suna daka mana harara.
Iyaye Na Guduwa Suna Barin ‘Ya’yansu
Wata ‘yar Burtaniya da ta tsere wa rikicin Sudan ta bayyana yadda aka dauke ta daga kasar lokacin da take tsakiyar ‘ya’yan yayyenta wadanda suke kuka, suna rirrike ta domin kada ta tafi, ta bar su.
Waafa Salim ta tattauna da BBC a filin jirgin Larnaca da ke Cyprus, inda jiragen Burtaniya ke sauka bayan sun taso daga Sudan gabanin su karasa kasarsu.
Ba a amince mata ta tafi da yaran ba saboda dokokin da Burtaniyan ta shimfida na kwaso mutanen.
“Ala dole, na mika su ga mahaifinsu. Wani mummunan lokaci ne da ba zan manta da shi ba,” in ji ta.
‘‘Kananan yara ne da ba su da kariya, kamata ya yi a ce an bari ni na taho da su cikin jirgi.
‘‘Sun shaida min cewa ba zan iya dauko su ba saboda ka’idar da aka sanya, sai mai fasfo din Burtaniya ne kawai za a dauka.
Na roke su na ce ‘ya’yana ne, amma suka ce hakan ba zai yiwu ba.”
Fadar mulki ta Downing Street ta zayyana wasu sharudda wadanda ta ce ba za a sauya su ba, amma an bai wa jami’an da ke Sudan, wuka da nama game da yanke shawara kan abin da suke gani ya fi zama daidai bisa la’akari da abin da ke faruwa zahiri a Sudan.
Ofishin wajen Burtaniya ya ce jirage takwas da suka tashi sun kwaso mutum 897 daga kasar wadda ke gabashin Afrika zuwa Cyprus a ranar Alhamis.
Amma duk da haka wannan wani adadi ne da bai taka kara ya karya ba bisa la’akari da yawan ‘yan Burtaniya da ke Sudan.
Waafa Salim wadda ma’aikaciyar tsare-tsare ce a wani ofis a Buckinghamshire, ta je Arewacin Sudan ne, inda ta ce mutane na samun tallafi daga Kungiyar Ba Da Agajin ta Red Cross.
Ta je Sudan ne da danta Hasan mai shekara 12, wata ziyara da ta kai wa ‘yan uwanta a lokacin Sallah karama.
Ya kamata a ce sun koma Burtaniya a makon jiya, amma yakin da aka fara ya haifar musu da tsaiko.
Ana Ganin Abubuwan Firgici Da Tashin Hankali
Ta samu damar tsallake shingen duba ababen hawa da yawa da danta ga kuma dan’uwanta, tare da ‘ya’yansa da ke tsakanin shekara 3 -10.
Sai dai, bayan ta tattauna da jami’an Burtaniya ne sai aka mayar da dan’uwanta da ‘ya’yan nasa.
“A dokar da suka bayar sun ce ‘ya’yan cikinmu kawai za mu iya fita da su,” in ji ta.
“Wadannan yaran da ba su san komai ba, ku bar su tare da ni. Shi dan’uwana ya zauna, amma suka ki.”
Ta ce yanzu dan’uwan nata da iyalansa na kokarin barin Sudan ta kan iyakar Masar, ta kara da cewa da babu yara da tafiyar ta fiye masa sauki.
A yanzu haka, duk wani mai fasfo din Birtaniya da iyalansa ko kuma mai shaidar zama a kasar zai iya samun damar a dauke shi.
Da yake magana tun da farko, sakataren wajen Burtaniya James Cleberly ya ce kada a bar duk dan Sudan din da ba shi da takardun zama a Burtaniya ya wuce shingen tantance mutane.
“Lokacin da aka samu dan Burtaniya na auren ‘yar Sudan kuma suna da ‘ya’ya, sai mu rasa yadda za mu yi,” in ji shi.
“Ya shawarci ‘yan Burtaniya su gaggauta tattara nasu ya nasu su fice daga Sudan domin ba a san me zai faru ba, idan lokacin yarjejeniyar tsagaita wuta ya kare.
Jami’ai a Burtaniya suna ci gaba da tuntubar bangarorin biyu da ke gaba da juna, a kan su daure su tsawaita wannan yarjejeniya ta tsagaita wuta tsakaninsu.
Da yake magana a gaban majalisa, sakataren waje na jam’iyyar adawa, Dabid Lammy ya yi kira ga gwamnati ta bari a kwashe ‘yan Sudan masu shaidar zama a Burtaniya.
A tare da Waafa Salim akwai danta mai shekara 12 Hasan, wanda ya rika fama da karancin barci a makon jiya saboda tashin bam da karar harbe-harben bindiga.
Ta ce abin takaici ne ka bar ‘yan’uwanka, cikin wannan matsala.
An shaida wa BBC cewa sai da aka kai Waafa Salim asibiti saboda rashin lafiya da ta kama ta a cikin jirgin sama.