Daya daga cikin ’yan jam’iyar A P C kuma mai sharshi a kafafan yada labarai na Jihar Kano, Alhaji Danjuma Bakin Wafa, a hirarsa da Wakilnmu, inda ya bayyana bacin ransa dangane da wasu abubuwa da su ka damu Nijeriya da batun jagorancin APC na kasa, inda ya ce bai wa gwamna mai ci bai dace ba.
Idan dai za a iya tunawa, a kwanakin baya ne jam’iyyar APC ta nada Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, rikon shugabancin jam’iyyar bayan rushe tsofaffin shugabannin a karkashin jagorancin Mista Adams Oshiohmole.
Ya ce, “gwamna ya na fama da jiharsa kuma a dauki wani aiki mai nauyi a dora ma sa, to da me zai ji? Wannan kuskure ne ai kawai, alhali ga mutane a zaune masu kokari irinsu Abdurraman Kawu Sumaila za su iya rike jam’iyyar.
“Ni a ganina wannan ba daidai ba ne. kamata ya yi a sa wanda za a bai wa rikon ba gwamna ba. Yanzu wannan gwamnan idan ka dubi jihar da ya fito, aikin da ke gabansa ya yi yawa. Wannan jam’iyar ya kamata a dauke ta a bai wa wanda ya ke da sukuni.”