Tawagar ‘yan wasannin Najeriya ta samu ƙarin lambobin yabo a gasar haɗin kan Musulunci ta shida, wacce ake kira Riyadh 2025 a Saudiyya, bayan lashe zinare, azurfa da tagulla biyu a daren ranar Laraba a filin wasa na Prince Faisal Bin Fahd da ke Riyadh.
‘Yan wasa mata huɗu daga Najeriya da suka haɗa da Iyanuoluwa Toyin Bada, Oluebube Miracle Ezechukwu, Maria Thompson Omokwe da Chioma Cynthia Nweke, sun lashe tseren 4×100 na mata da maki 44.27.
- ’Yan Bindinga Sun Sace Mutane 9, Sun Raunata 1 A Sakkwato
- Ba Za A Yarda Da Farfado Da Dabi’ar Japan Ta Amfani Da Karfin Soji Ba
Bahrain ta samu azurfa da maki 44.47, yayin da Gambiya ta samu tagulla da maki 45.05.
A tseren 4×100 na maza, ‘yan wasa Nijeriya Caleb John, Chidera Ezeakor, Ezekiel Eno Asuquo da James Taiwo Emmanuel sun samu tagulla da maki 39.52.
Masu masaukin baƙi Saudiyya ta samu zinare da maki 39.19, yayin da Oman ta samu azurfa da maki 39.21.
Hakazalika, a daren ranar Laraba Patience Okon-George ta samu azurfa a wasan gudun mita 400 na mata da maki 51.93.
ZSalwa Eid Naser daga Bahrain ta samu zinari da maki 51.59, tagulla kuma ta tafi hannun Leni Shida daga Uganda da maki 52.72.
Samuel Adams Kure ya samu tagulla a wasan Javelin na maza.
Da wannan, Nijeriya tana matsayi na 9 a kan teburin lambobin yabo, da jimillar lambobin yabo 25: zinare takwas, azurfa 10, tagulla bakwai.
Turkiyya na kan gaba da zinare 68, azurfa 42 da tagulla 38; Uzbekistan ta biyu da zinare 26, azurfa 30 da tagulla 26; Iran ta uku da zinare 21, azurfa 18 da tagulla 25. Masaukin baki Saudiyya tana matsayi na bakwai da zinare 11, azurfa 6 da tagulla 22.














