A yau Talata ne aka yi wa Cristiano Ronaldo tarba ta girmamawa a Hong Kong inda yaje domin wakiltar Al Nassr a wasan da suka doke Al Ittihad. Wannan birnin ne dai a bara suka bayyana Lionel Messi a matsayin makiyinsu bayan ya kasa buga wasan da aka shirya gudanarwa tareda kungiyarsa ta Inter Miami. Tsohon dan wasan Manchester United da Real Madrid Ronaldo, mai shekaru 40 ne, ya bayar da kwallon da Joao Felix ya ci a wasan kuma wadda ta samarwa Al Nassr nasara.
“Ronaldo, Ronaldo,” shi ne abinda dubban magoya baya ke fadi yayin da filin wasan dake Kudancin China ya yi cikar kwari, har ma wasu masoyan sun so su hada jikinsu da gwarzon dan wasan kafin jami’an tsaro su hana, akan barke da ihu a duk lokacin da kyaftin din na Portugal, sanye da riga mai lamba bakwai, ya taba kwallo.
A watan Fabrairun bara ne Messi ya ki ya shiga wasan sada zumunta da aka shirya bugawa da Inter Miami a Hong Kong, dan kasar Argentina din ya bata rayuwar dubban magoya bayansa da suka biya makudan kudade don ganin kyaftin din da ya lashe kofin duniya ya buga wasa, duk da cewa dan wasan mai shekaru 38, ya ce ya samu rauni amma hakan ya janyo soke wasanni biyu da China ta shirya bugawa da kasar Argentina.
Messi da Ronaldo sun shafe fiye da shekaru 15 suna jan ragamar kyautar gwarzon dan wasan duniya da ba a hukumance ba, duk da cewa ana kallon dan wasan na Argentina a matsayin wanda ke kan gaba, dukansu sun kasance shahararru a wannan bangare, Ronaldo ya zura kwallaye biyu a raga saura minti shida a tafi hutun rabin lokaci amma an hana shi a duka biyun.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp