Roxy Danckwerts, shugaba ce a sansanin kare namun daji na kasar Zimbabwe. Yayin ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a Zimbabwe a shekara ta 2015, Roxy ta gabatar masa da ire-iren dabbobin dake wurin.
Abun da ya fi burge Roxy a yayin tattaunawarta da shugaba Xi shi ne, yadda ya maida hankali sosai gami da lura da ayyukan da suka shafi kare dabbobi, da fahimtar kalubalolin da ake fuskanta a fannin kare su.
Kaza lika, shugaba Xi ya ba Roxy kyautar wata kwalbar furanni mai zanen dabbar Panda ta kasar Sin, da bayyana mata shirin kiwon Panda da kasar Sin ke aiwatarwa yanzu.
Roxy ta ce tana matukar son rungumar Panda, kuma a ganinta, a karkashin jagorancin shugaba Xi, ayyukan kiyaye namun daji na kasar sun samu babban ci gaba, kana kuma saboda kulawarsa, ayyukan kiyaye namun daji sun sake zama babban abun dake jan hankalin duk duniya. (Murtala Zhang)